Bankin FCMB ya dauki nauyin karatun dalibar da take rubuta jarrabawa a gaban bankin da daddare

Bankin FCMB ya dauki nauyin karatun dalibar da take rubuta jarrabawa a gaban bankin da daddare

- A kwanakin nan ne hotunan wata karamar yarinya tana amfani da hasken ATM da dare don yin aikin makarantarta ya zagaye kafar sada zumunta

- Bayan wani ya ga yarinyar tana aikin, sai ya dau hotonta tare da wallafawa a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita

- Bankin FCMB kuwa sun nemi yarinyar don a halin yanzu sun dau nauyin karatunta kamar yadda jaridar Within Nigeria ta wallafa

Dele karamar yarinya ce ‘yar makaranta wacce aka ga tana amfani da hasken ATM din bankin FCMB wajen yin aikinta na makaranta. Mazauniyar jihar Ondo ce da kakarta, kuma hotunanta sun jawo cece-kuce a kafofin sada zumuntar zamani.

A yayin da karamar yarinyar ke amfani da hasken ATM din, wani ma’aboci amfani da kafar sada zumuntar zamani ta twitter ya ganta tare da daukar hotonta. Ya wallafa hoton wanda ya yadu a kafar sada zumuntar.

Bayan wannan hoton ya kai ga hukumar bankin ne, sai suka nemi a nemo musu inda zasu ga Dele yadda zasu dau nauyin karatunta, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta wallafa.

KU KARANTA: Nasarar kowanne mai arziki na duniya na da alaka da wanda ya zaba a matsayin abokin rayuwa - Bincike

Kamar yadda ya wallafa: “Na ga karamar yarinyar nan mai suna Dele a kan titin Yaba da ke birnin Ondo. Tana amfani da hasken ATM ne don yin aikin da aka ba ta a makaranta. Na mutunta jajircewarta da nacinta.”

Sai hukumar bankin suka mayar da martani ta shafinsu na tuwita kamar haka: “A gaskiya mun lura tana da son karatu. Muna farin ciki ta yadda ATM dinmu ya zama haske gareta, amma zamu so taimakonta. Za ka iya nemo mana Dele? A yi ta wallafawa har ya kai ga inda aka santa.”

Rahotanni da yawa sun tabbatar da cewa Dele na zama ne tare da kakarta kuma an gano su. A halin yanzu tana zuwa wata makaranta ne mai suna Hope of Glory Academy a Ondo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel