Dubu 600 nake samu duk wata da sana'ar acaba - Cewar wata mata da take acaba a Legas

Dubu 600 nake samu duk wata da sana'ar acaba - Cewar wata mata da take acaba a Legas

- Wata mata mai sana’ar achaba ta koka da irin illar da hana sana’ar achaba da gwamnatin jihar Legas tayi, ta mata

-Matar ta bayyana cewa a kalla a rana daya tana yin naira dubu ashirin a wannan sana’ar kuma ita daliba ce a wata makarantar gaba da sakandire ce a kasar nan

- Gwamnatin jihar ya bayyana cewa daukan wannan mataki yana daya daga cikin tsare-tsarenta na tsaftace hanyoyin cikin garin Legas

Wata mata mai sana’ar achaba ta bayyana irin arzikin da take samu a sana’arta. Tana daya daga cikin wadanda suka fita zanga-zanga akan yadda gwamnatin jihar Legas ta haramta achaba. Hakan yasa suka fita don nuna rashin amincewarsu da hana achaban da gwamnatin jihar tayi.

A yayin zantawa da manema labarai yayin zanga-zangar, matukiyar ta ce tana karatu ne a wata makarantar gaba da sakandire a kasar nan kuma tana samun a kalla naira dubu ashirin a kowacce rana daga achabar da take yi.

Dubu 600 nake samu duk wata da sana'ar acaba - Cewar wata mata da take acaba a Legas
Dubu 600 nake samu duk wata da sana'ar acaba - Cewar wata mata da take acaba a Legas
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da hukuncinta na haramta achaba da kuma yawo da adaidaita sahu a lunguna da sakonni jihar har 15 daga ranar 1 ga watan Fabrairu na 2020, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Legas ta haramta sana'ar tuka babur mai kafa biyu, watau 'Achaba', da babur mai kafa uku, da aka fi sani da 'adaidaita', a fadin kananan hukumominta guda shidda (LCDAs).

KU KARANTA: Ikon Allah: Harsashi ya kashe ta amma dan cikinta ya rayu

Kananan hukumomi 6 da sabuwar dokar ta shafa sune kamar haka; karamar hukumar Apapa da Apapa Iganmu, Lagos Mainland da Yaba LCDA a karamar hukumar Surelere, Itire-Ikate da Coker Aguda LCDAs, karamar hukumar Ikeja da Onigbongbo da Ojodu LCDAs.

Sauran sune; karamar hukumar Eti-Osa, Ikoyi-Obalende da Iru/Victoria Island LCDAs, karamar hukumar Lagos Island da Lagos Island ta gabas LCDA.

A cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa dokar zata fara da karfinta daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2020.

Gwamnatin jihar ya bayyana cewa daukan wannan mataki yana daya daga cikin tsare-tsarenta na tsaftace hanyoyin cikin garin Legas da kuma kare jama'a daga illolin da wadannan hanyoyin sufuri (Achaba da adaidaita) ke haifar wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel