Rikicin ma’aurata: Magidanci ya daure matansa 2 da mari tsawon watanni 10 a Katsina

Rikicin ma’aurata: Magidanci ya daure matansa 2 da mari tsawon watanni 10 a Katsina

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta sanar da kama wani mugun magidanci mai suna Samaila wanda ake zarginsa da cin zarafin matansa guda biyu ta hanyar dauresu da kaca tsawon wata da watanni.

Punch ta ruwaito Samaila mazaunin kauyen yan Nabaiyye cikin karamar hukumar Rimi ta jahar Katsina ya daure matan nasa biyu da suka hada da Fatima Salisu da Hadiza Musa, wanda shekarunsu basu wuce ashirin ashirin ba.

KU KARANTA: Za’a samu tsaro idan muka kawar da bambancin dake tsakaninmu – Buhari ga yan Najeriya

Rikicin ma’aurata: Magidanci ya daure matansa 2 da mari tsawon watanni 10 a Katsina
Hadiza Fatima
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Samaila ya daure Malam Fatima da kaca ne tsawon watanni 10, yayin da ya daure Hadiza tsawon watanni 10, kamar yadda rundunar Yansandan jahar Katsina ta tabbatar, ta bakin kaakakinta, SP Gambo Isah.

Ita dai Fatima yar asalin kauyen Marken Magaji Gari ne, yayin da Hadiza kuma yar asalin kauyen Kalyarubandaba ne, kuma dukkaninsu basu taba samun haihuwa da wannan mutumi ba.

Mahaifiyar Hadiza ce ta fara gano halin da diyarta da abokiyar zamanta suke ciki yayin wani ziyara da ta kai gidanta ba tare da sanar da ita ba, inda ta tafi daukan keken dinkin da ta saya ma diyarta, amma sai mijin ya hanata dauka, hakan yayi sanadiyar cacar baki tsakaninsu, inda ya doketa.

Wannan ne yasa matar ta garzaya ofishin Yansanda dake cikin karamar hukumar Rimi domin kai korafi, daga nan sai Yansanda suka gayyaci Samaila domin amsa tambayoyi, sai dai basu gamsu da bayanansa ba, don haka suka tafi gidansa domin gudanar da bincike.

A sanadiyyar wannan bincike ne Yansanda suka gano matan biyu daure da kaca cikin mawuyacin hali har sun fita hayyacinsu, haka zalika Yansanda sun gano manyan mari, layoyi da kuma muggan makamai.

A cewar Fatima, bayan Samaila ya dauresu, sa’annan ya aske musu gashin gaba da kuma yanke musu kumba wanda yayi amfani dasu wajen hada wani jiko, kuma ya tilasta musu su sha.

“Samaila baya barinmu mu fita ko ina, a daure muke fitsari muke kashi, baya kwancemu sai lokacin da yake bukatar saduwa damu, haka muke kallo a duk lokacin da yake saduwa da wani daga cikinmu, haka zalika yana dukanmu da wayar wuta.” Inji ta.

Bugu da kari Hadiza ta ce Samaila baya son jin lokacin da muke jinin haila, saboda a duk lokacin daya gane muna jinin haila duka ne zai biyo baya tare da barazanar kashe mu, sai dai tace basu san sana’arsa ba, amma dai suna ganinsa kullum yana dawowa gida da yan dari biyar biyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel