Amfanin cin dafaffen kwai guda 7 a jikin mutum

Amfanin cin dafaffen kwai guda 7 a jikin mutum

- Ba yara kadai kwai yake wa matukar amfani ba a lokacin tasowarsu, har da manya

- Kwai yana kunshe da sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar dan Adam

- Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana don yana dauke da Vitamin D

Ga yara kwai a lokacin da suke tasowa na da matukar amfani domin yana inganta girman jikin yaran saboda sinadarorin da kwan ke dauke da shi.

Kwararru sun nuna cewa kwai na dauke da sinadarorin Vitamin A, B12, D, B6 wanda ke taimakawa wajen kara karfin garkuwan jiki yara musamman ‘yan kasa da shekaru 5.

1. Dafaffen kwai na bude kwakwalwan yaro.

2. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin ‘lutein’ and ‘zeaxanthin’ wanda ke kara lafiyar idanuwan yaro.

3. Dafaffen kwai na kara karfin kashi a jikin yara kanana domin yana dauke da sinadarin Vitamin D.

KU KARANTA: Tirkashi: Boka ya dirkawa matar fasto cikin shege

4. Dafaffen kwai na dauke da sinadarorin leucine, phenylalanine, histidine, isoleucine, lycine, methionine, threonine, tryptophan da valine wadanda ke taimakawa wajen gina jikin yaro da kuma kara masa jini.

5. Dafaffen kwai na kara girman kunba da gashin kan yara.

6. Omega-3 da ke cikin dafaffen kwai na taimakawa wajen bude kwakwalwar yaro kuma zai yi saurin gane abubuwa.

7. Dafaffen kwai na dauke da sinadarin Iron da ke taimakawa wajen samar da issashen jini a jikin yaro Wanda rashin shi yakan sa aga yaro na kumbura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng