Amfani 10 da kukumba ke yi a jikin dan adam
Amfanin cin danyen gurji suna da yawa kamar yadda wani masanin ilimin hada magunguna mai suna Gurama Gurama A. ya bayyana. Cucumber na daga cikin dangin kayan marmari daga cikin rukunin Cucurbitaceae kuma tana kunshe da ruwa mai tarin yawa.
Gurama yace cucumber na taimakawa wajen rage rashin ruwa a jiki ballantana a lokutan zafi.
"Mutane na cin cucumber ne a matsayin kayan lambu amma tana cikin kayan marmari. Ana amfani da ita a cikin wasu kayayyakin gyaran fata. Kayan marmari ce kamar kankana da kabewa." In ji shi.
Tana kunshe da sinadaran Vitamin irinsu A, B, C, K, potassium da Manganese wadanda ke da matukar amfani a jikin dan Adam.
Ga wasu daga cikin amfanin cucumber kamar yadda Gurama ya bayyana.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano
1. Tana taimakawa wajen narkewar abinci.
2. Tana taimakawa wajen rage kiba.
3. Tana taimakawa wajen karin lafiyar kwakwalwa.
4. Gurji na warware gajiyar jiki.
5. Gurji na kunshe da sinadaran vitamin B1, B5 da B7.
6. Tana hana warin baki da fitar numfashi.
7. Gurji na hana ciwon koda.
8. Gurji na maganin ciwon ido.
9. Gurji na taimakwa wajen daidaituwar karfin bugawar jini daga zuciya.
10. Akwai yiwuwar gurji ta kare mutum daga cutar sankara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng