Darektan hukumar kwana - kwana ta Kano ya mutu
A ranar Talata ne aka binne gawar Malam Sagir Madaki, darektan hukumar kwana -kwana ta jihar Kano, a makarbatar Dandolo dake unguwar Goron Dutse a yankin karamar hukumar Gwale.
Jaridar Solabase dake Kano ta rawaito cewa wani dan uwa ga marigayin mai suna Ibrahim Umar ya ce Malam Sagir Madaki ya mutu ne da yammacin ranar Talata a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan takaitacciyar rashin lafiya.
An yi masa sallar jana'iza bisa tsarin addinin Musulunci a unguwar Yola dake cikin birnin Kano, a yammacin ranar Talata.

Asali: Twitter
Daga cikin wadanda suka halarci jana'izar marigayin akwai kwamishinan aiyuka na jihar Kano, Mu'azu Magaji.
Marigayi, Malam Sagir Madaki, ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya bakwai.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng