Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Dubai

Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Dubai

- Wani dan Najerya mai suna Obinna dan asalin jihar Anambra ya bayyana yadda yake sana’ar gasa masara a Dubai

- Ya yanke shawarar fara sana’ar gashin masara ne bayan da ya rasa aikin yi, kuma ya gano ba yadda ake yi a Najeriya suke yi ba

- A halin yanzu yana samun Dirhami 60 zuwa 80, wanda yayi dai-dai da dubu takwas a ko wacce rana

Wani dan Najeriya mai suna Obinna ya dage da sana’a don samun madogara a rayuwarshi yayin da yake zama a Dubai. Obinna dai ya rungumi sana’ar gasa masara ne don dogaro da kanshi a kasar da ba tashi ba.

Kamar yadda wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook ya wallafa, yace Obinna dan asalin jihar Anambra ne ta Najeriya. Ya koma Dubai tare da rike sana’ar gasa masara bayan da yayi kokarin samun aiki amma ya kasa.

Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Landan

Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Landan
Source: Facebook

Obinna da kanshi ya bayyana yadda wannan abu ya fara.

“Sunana Obinna, daga Njikoka ta jihar Anambra a Najeriya. A lokacin da na isa Dubai kuma na kasa samun aikin yi, sai na fara tunanin wacce sana’a zanyi don samun rufin asiri.

KU KARANTA: Hadiza Gabon ta mayarwa da wani saurayi da ya dade yana nemanta da aure martani

“Wata rana yayin da naje wani wajen cin abinci, wani mutum ya shigo tare da mika bukatar abincin da yake so. Kaza ya bukata tare da faten dankali da kuma gasassar masara. Amma wannan masarar ba a gasa ta kamar yadda muke yi a Najeriya ba.

“Daga nan ne na fara tunanin gwadawa. Na nemi wani manomi da zai dinga kawo min masarar danya, kuma na fara sana’ar gasa masarar a kusa da inda nake zama.

Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Landan

Hotuna: Dan Najeriya dake sayar da gasasshiyar masara a birnin Landan
Source: Facebook

“Da farko mutanen kan wuce suna kallona don basu taba ganin ana gasa masara da garwashi ba. Watarana sai na ba wani mutum guda daya don ya dandana. Daga nan ne ya fara kawo min mutane masu siya. A halin yanzu ina samun Dirhami 60 zuwa 80 a kowacce rana. Daidai yake da dubu takwas kullum.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel