Ba zai yuwu 'yan Najeriya su cigaba da zuwa asibitocin kasashen ketare ba - Buhari

Ba zai yuwu 'yan Najeriya su cigaba da zuwa asibitocin kasashen ketare ba - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a, ya ce 'yan Najeriya ba za su cigaba da zuwa kasashen ketare don neman magani ba, kamar yadda jaridar The Punch ta bayyana. "Yan Najeriya suna wahala wajen tafiya kasashen ketare don neman lafiya. Wannan bai dace da mu ba, kuma dole mu dena saboda bamu da kudin cigaba da yin hakan," in ji shi.

Idan zamu tuna, ba sau daya ko biyu bane shugaban kasar yake garzayawa Amurka don neman lafiya. Ya sanar da hakan ne a asibitin koyarwa na jami'ar tarayya ta Alex Ekwueme da ke Abakaliki, yayin kaddamarwa tare da mika wasu aiyuka ga hukumar asibitin.

Ya bayyana cewa, anyi aiyukan ne don shawo kan ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa dake addabar asibitin.

Shugaban kasar, wanda ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu ya wakilta, ya koka da yadda ambaliyar ruwan ta addabi yankin Kudu maso gabas din. Ya ce an yi wadannan aiyukan ne don kawo sassauci ga asibitin, jihar da kuma makwabtanta.

DUBA WANNAN: Yadda Dangote ya zama dan Afirka tilo cikin jerin mutane 100 mafi arziki a duniya

Ya ce wadannan aiyukan da aka yi a jihar na nuna alamun shudewar zamanin zaben yankunan da za a dinga wa aiki a kasar nan, saboda rashawa da son kai da yayi katutu. Ya jaddada cewa, yin wannan aikin a yankin na nuna cewa ba za a bar ko ina a baya ba a fadin kasar nan.

Ya ce, "Mun mayar da hankali wajen kiwon lafiyar jama'armu kuma zamu cigaba da yin hakan. Wannan aikin da muke murnar kammalawa a yau, ya shafi wasu ayyukan aisbitin nan masu dumbin yawa. Amma a yau zamu ce kammalar shi ya fara shafar cigaban wasu manyan aiyuka, ma'aikata da kuma majinyatan asibitin nan."

"Ina so inyi amfani da wannan damar wajen taya sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha murna, 'yan kwangilar, Messrs Amayaro Nigeria Limited da sauran wadanda suka tabbatar da kammaluwar wannan aikin." in ji ministan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel