Magoya bayan Atiku ne ke son kasheni kafin zaben 2023 - Jigon PDP

Magoya bayan Atiku ne ke son kasheni kafin zaben 2023 - Jigon PDP

- Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ya bayyana cewa ana barazana ga rayuwarshi

- Sanata Walid ya ce a kan kira shi a waya tare da ja mishi kunne a kan zancen yankin da zasu ba tikitin takarar shugaban kasa a PDP

- Ya bayyana cewa, wasu magoya bayan tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ne ke mishi wannan barazanar

Shugaban kwamitin yardaddu na jam'iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ya jawo hankulan jama'a ta yadda magoya bayan tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ke barazana ga rayuwarshi a kan tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar a 2023.

Ya sanar da hakan ne a zantawar da yayi da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu.

"Ina samun kiran waya daga wasu mutane masu barazana ga rayuwata a kan yankin da ya kamata a ba takarar shugaban kasa. Sun ce na ci amanar yankin Arewa maso gabas kuma da Atiku kadai nake."

KU KARANTA: Tsananin sanyi ya hana mutane fita aiki a garin Jos

"A halin yanzu ba mu tattauna a kan yankin da za a ba takara ba, a kan me suka damu da inda za a ba tikitin? Wasu mutane uku sun zo jerin kantuna na Wadata kuma sun bukaci gani na. An kirani a waya na shaida musu ina Kaduna. Sai suka sanar cewa wasu 'yan siyasa ne suka turo su. Matukar ban shiga taitayina ba, zasu hada 'yan ta'addan da zasu yi min aika-aika.

"A take nace musu suje suyi abinda duk zasu yi, na shirya. Daga nan ne na gano cewa suna nufin kasheni ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel