Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria

Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria

A wani mataki da za’a iya kira basabamba, bangaren dokoki na karamar hukumar Zaria ta jahar Kaduna daya kunshi majalisar zababbun kansilolin karamar hukumar ta sanar da tsige shugaban karamar hukumar Zaria, Injiniya Aliyu Idris Ibrahim.

Kansilolin sun bayyana haka ne cikin wata wasika da suka aika ma shugaba Aliyu Idris ta hannun sakataren karamar hukumar inda suka ce sun yi haka ne duba da tanadin sashi na 9(1), (2), (3) da (4) na kundin dokokin jahar Kaduna.

KU KARANTA: Siyasa rigar yanci: Dan majalisa ya baiwa mutane 220 mukamin masu bashi shawara

Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria

Siyasar Kaduna: Majalisar Kansiloli ta tsige shugaban karamar hukumar Zaria
Source: Facebook

Wasikar da ta samu sa hannun kwansiloli guda 10 cikin kansiloli 13 dake wakiltar mazabun karamar hukumar Zaria ta bayyana cewa wadannan sassa na kundin tsarin mulki sun baiwa kansiloli daman sanar da shugaban karamar hukuma kafin su tsige shi ta hanyar mika masa takarda ta hannun sakatare.

Daga cikin kansilolin da suka rattafa hannu kan takardar tsigewar kamar yadda wasikar take dauke da sunayensu akwai: Yushau Muhammad Inuwa daga Anguwar Fatika, Akilu Abubakar daga Kufena, Musa Salisu daga Tudun Wada, Salisu Ibrahim daga Kaura da Ismail Shuaibu Tukur Tukur.

Sauran sun hada da Honorabul Aminu daga Gyallesu, Salisu Magaji daga Likona, Ibrahim Sambo kansilan mazabar Kwarbai B da kuma kansilan Anguwar Juma, dukkaninsu sun rattafa hannu a kan wannan takarda.

A yayin zantawarsu da manema labaru, mai magana da yawun kansilolin ya bayyana cewa suna tuhumar shugaban da aikata laifuka da dama da suka hada da yi karan tsaye ga dokokin bayar da kwangila na jahar Kaduna, almubazzaranci da kudin al’umma, yi ma dokar kasafin kudi kaca kaca da sauran laifuka da dama.

A wani labarin kuma, wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Akoko ta Arewa maso gabas da Akoko ta Arewa maso yamma a majalisar wakilan Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya dauki mutane 220 aiki a matsayin hadimansa da zasu taya shi aiki.

Mai magana da yawun dan majalisan, Alao Babatunde ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 1 ga watan Disamba inda yace Olubunmi ya nada shugaban ma’aikatansa guda 1, mashawarta na musamman guda 6, mataimaka na musamman guda 156 da kuma hadimai 67.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel