An rubuta kalaman kyamar musulunci a jikin wani masallaci a London

An rubuta kalaman kyamar musulunci a jikin wani masallaci a London

- A wani gini dake da kusanci da wani masallaci dake Kudancin birnin London ne aka zana taken da ke nuna kyama ga addinin Musulunci

- Jami'an tsaron yankin sun ce ana aiki da karamar hukumar Lambeth domin cire kalaman daga wajen

- Magajin garin London ya wallafa cewa, babu shakka za a gano wadanda suka yi wannan aika-aikar kuma za su fusknaci hukunci

A wani gini dake da kusanci da wani masallaci ne da ke Kudancin birnin London aka zana taken da ke nuna kyama ga addinin Musulunci.

An gano wannan alamar ne a jikin wani gini a kusa da cibiyar addini dake kan titin Brixton da karfe 11:00 agogon GMT.

Jami'an tsaron yankin sun ce suna aiki da karamar hukumar Lambeth domin cire "kalaman batancin" daga jikin ginin da gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Soja mafi tsufa a Najeriya ya rasu yana da shekara 101 (Hotuna)

Hukumar 'yan sandan ta kara da cewa, tana gudanar da bincike don gano wanda yake da hannu a wannan aika-aikar.

Sadiq Khan ya ce, bai ji dadin ganin rubutun ba wanda aka manna a ginin bayan kwanaki kadan da aka manna kalaman batanci ga Yahudawa, a shaguna da wurin ibadar Yahudawan a Arewacin birnin London.

Magajin garin London ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter. Ya ce: "Duk kalaman nuna wariya, alama ce ta tsoro kuma masu laifin zasu fusknaci fushin hukuma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel