Tirkashi: An yankewa tsoho hukuncin daurin rai da rai akan ya saci N3,000

Tirkashi: An yankewa tsoho hukuncin daurin rai da rai akan ya saci N3,000

- Simmons dattijo ne bakar fata mai shekaru 62 wanda ke gidan yari a Alabama na tsawon shekaru 38

- Ya zargi kotu da rashin mishi adalci saboda ta yanke mishi hukuncin zaman gidan yari na tsawon rayuwarshi ne sakamakon satar $9 da yayi

- Ya bayyana yadda aka yanke mishi hukunci cikin mintuna 25 ba tare da sauraron shaida daga bangarenshi ba saboda shi baki ne

AL-Willie Simmons dattijo ne mai shekaru 62 kuma bakar fata daga Alabama. Ya yi shekaru 38 a gidan yari saboda satar $9. Alkalin ya yanke mishi hukuncin sata babu tara tun a 1982.

Beth Shelburne wani dan jarida ne mai aiki da WBRC, ya bayyana labarin Simmons a shafinshi na tuwita kamar yadda ya tattauna da shi.

Simmons ya sanar da Shelburne cewa ya kasance a nan tun yana da shekaru 25 kuma akwai yuwuwar zai mutu a nan tunda bai sake yin bako ba tun 2005 da 'yar uwarshi ta rasu.

A halin yanzu yana da shekaru 62 a duniya kuma yana ajiye ne a gidan gyaran hali na Holman dake Escambia County, Alabama. Wannan gidan gyaran hali ne kuwa da yafi kowanne tashin hankali a kasar.

Simmons bai musanta laifin da yayi ba har ya dangana da gidan yari. Ya dai tabbatar da cewa ya sha kwaya ne lokacin da yayi dambe da wani mutum har ya kwace mishi jakarshi dake dauke da $9.

KU KARANTA: Innalillahi: Dan kwallon Najeriya ya bayyana yadda ya kashe kanwarsa yayin da take dauke da tsohon ciki

Simmons yace an yanke mishi hukunci ne cikin mintuna 25. Lauyanshi kuwa bai kira wata shaida ba kuma masu gurfanarwa basu karba ban hakurin da aka yi a kan laifinshi ba. "Suna ta cewa, zamu yi iyakar bakin kokarinmu don dauke ka daga titi," ya ce.

A cikin shekarun da suka gabata, ya dade yana yunkurin daukaka kara duk da bashi da lauya amma an hana shi.

'Yan majalisar kasar a 2014 ne suka cire damar daukaka kara ga wadanda aka yankewa hukuncin kisa kamar Simmons. Amma kuma Simmons na fatan wannan mummunan hukunci zai dage wata rana. "Eh, ina fata kuma ina ta addu'a a kan hakan. Ban cire rai ba," ya ce.

Hakazalika, Simmons yana fatan wata rana za a sake shi kuma yayi rayuwarshi kamar kowa.

"Fatana shine in fita daga nan, inyi aure tare da zama lafiya," in ji shi.

"Ina so in sanar da mutane mummunan illar miyagun kwayoyi." Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel