Jagoran yan bindiga ya bayyana yadda haduwarsa da kwamishinan Yansanda a daji ta kasance

Jagoran yan bindiga ya bayyana yadda haduwarsa da kwamishinan Yansanda a daji ta kasance

Tsohon kasurgumin dan bindiga, kuma shugaban tubabbaun yan bindigan jahar Zamfara, Muhammadu Bello ya bayyana yadda haduwarsa ta kasance da kwamishinan Yansandan jahar, Usman Nagogo a dokar dajin Shinkafi.

Bello ya bayyana cewa shi da yaransa a kan babura fiye da 80 dauke da muggan makamai suka hadu da kwamishinan da nasa yaran ba tare da suna dauke da ko tsinke ba, kamar yadda suka amince za’a yi haduwar, “Tun daga nan na fahimci da gaske su ke.” Inji shi.

KU KARANTA: Shugaba nagari: Buratai ya kai ma Sojoji ziyara a filin daga

Daily Trust ta ruwaito Bello ya bayyana haka ne yayin zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki a fadar Sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammadu Makwashe Isah, inda aka hadu don duba nasarorin da aka samu tun bayan kirkiro tsarin afuwa ga yan bindiga, tare da nazari game da kalubalen da aka fuskanta.

“Yan bindiga fiye da 80 a kan babura ke tare da ni a lokacin da na hadu da kwamishinan Yansanda tare da kwamishinan tsaro, Alhaji Abubakar Dauran a cikin daji, a lokacin sai da yarana suka nemi kada na sake na je, saboda basu yarda da su ba, suna zargin tarko aka shirya min.

“Amma na ce musu kada su damu, idan ma tarko ne, na amince na fada cikinsa saboda na gaji da halin da ake ciki, muma muna son a kawo karshen matsalar, kuma tunda har an kawo tsarin zaman lafiya, gara mu rungumeta.

“Babu makamai a hannunsu a lokacin da muka hadu dasu, hakan ya nuna da gaske suke, kuma mun tattauna yadda za’a samar da zaman lafiya a jahar Zamfara. Da ikon Allah zaman lafiya ya dawo Zamfara, duk da dai muna sane da wasu da suka bijire, amma ba zasu yi nasara ba, ina kira ga manoma da makiyaya su mayar da wukakensu cikin kube.” Inji shi.

A nasa jawabin, kwamishinan Yansandan jahar, Nagogo ya bayyana cewa akwai nasarori da dama da aka samu a sha’anin tsaro a jahar Zamfara tun bayan fito da tsarin afuwa ga yafiya da yan bindigan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel