2020: Jawabin shugaban kasa na sabuwar shekara

2020: Jawabin shugaban kasa na sabuwar shekara

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara da yi wa ‘yan Najeriya godiya a bisa zabensa da suka sake yi a karo na biyu. Ya yaba wa abokan adawarsa da suka yi takara kuma suka rungumi sakamakon zaben da hannu bibbiyu.

Buhari ya kara da cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasa ba a 2023, amma kuma zai tabbatar da ingancin harkar zaben kasar nan.

Ya cigaba da maimaita aniyarsa ta yaki da rashawa, samar da tsaro, wadanda yace suna daga cikin alkawarin da yayi yayin gangamin neman zaben a 2015.

Sai da shugaban yace, duk da matsalolin da aka samu, amma dakarun kasar nan sunyi nasara a yayin yaki da mayakan Boko Haram, masu garkuwa da mutane da sauran masu laifuka. Ya yi alkawarin samar da tsaro mai inganci ta hanyar samar da kayan aikin zamani, da bai wa sojojin kasar nan horo na musamman.

DUBA WANNAN: Ban taba ganin shugaba mai bin tsarin demokradiyya kamar Buhari ba - Yahaya Bello

Shugaban ya kara jaddada alkawarin da yayi na yaye talauci daga Najeriya tare da tsamo miliyoyin matasan Najeriya daga talauci a tsawon shekaru 10.

Hakazalika, Buhari ya ce ma’aikata zasu samu albashin da zai ishe su, sannan su kuma ‘yan fansho zasu samu kulawa ta musamman.

Dangane da kasafin kudin shekarar 2020, Buhari yace kasafin zai taimaka wajen cika burinsa na gudanar da sauye-sauye a kasar nan. Ya kara da yiwa majalisar dattijai godiya karkashin shugabancin Ahmad Lawan kan amince wa da kassafin kudin ba tare da bata lokaci ba.

Sai dai shugaba Buhari ya yi wa tsohuwar majalisar dattawan karo na takwas shagube, “ba tare da wani dalili ba suka ajiye kasafin kudin har fiye da watanni bakwai kawai domin siyasa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel