Daga karshe: Buhari ya bayyana abinda zai yi bayan karewar wa'adin mulkinsa

Daga karshe: Buhari ya bayyana abinda zai yi bayan karewar wa'adin mulkinsa

Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya ce zai bar shugabancin kasa a 2023 kuma ba zai kara neman wata kujerar siyasa ba. Buhari ya tabbatar da cewa shi mai bin dokokin damokaradiyya ne kuma zai yi duk abinda ya dace don habaka tare da kare su a Najeriya da yankin Afirka ta Yamma.

Ya bayyana hakan ne a sakon jawabin sabuwar shekarar da fadar shugaban kasa ta saki da karfe 6 na safiyar yau Laraba, 1 ga watan Janairu na sabuwar shekarar miladiyya.

“Zan sauka daga mulki a 2023 kuma ba zan kara neman wata kujerar siyasa ba a nan gaba. Amma a shirye nake da in tsarkake tare da karfafa tsarin zaben Najeriya da fadin Afirka ta Yamma, inda da yawa daga cikin kasashen ECOWAS zasu yi zabe a wannan shekarar,” in ji shi.

DUBA WANNAN: Ban taba ganin shugaba mai bin tsarin demokradiyya kamar Buhari ba - Yahaya Bello

A wasikar mai taken ‘’Wasikar sabuwar shekara daga shugaban kasa”, kuma wacce ya sa hannu a kanta, yace fada da rashawa, habaka tattalin arziki da kuma yaki da rashin tsaro ne zai cigaba da tabbatarwa har zuwa karshen mulkinsa.

Wannan karin jaddada cewa zai bar ofishinsa a 2023, na bayyanawa karara cewa akwai shirye-shiryen samar wa da shugaban kasar zarcewa karo na uku bayan ya kammala mulkinsa a 2023, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel