Abdulmuminu Jibrin ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai ma shugaban kasa Buhari

Abdulmuminu Jibrin ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai ma shugaban kasa Buhari

Tsohon dan majalisa dake wakiltar Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibrin ya bayyana cewa ya kai ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara ne domin ya jinjina masa bisa namijin kokarin da yake yi da kuma nasarorin daya samu a mulkinsa.

A ranar Talata, 31 ga watan Disamba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Abdulmuminu Jibrin a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Dan majalisar wakilai daga jahar Jigawa ya rigamu gidan gaskiya

Abdulmuminu Jibrin ya bayyana dalilin ziyarar da ya kai ma shugaban kasa Buhari
Abdulmuminu Jibrin da Buhari
Asali: Facebook

A jawabinsa, Jibrin ya bayyana cewa ya ziyarci shugaba Buhari ne kamar yadda ya saba yi, kuma a wannan karo sun tattauna kan nasarorin da ya samu a shekarar 2019, musamman a fannin tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Haka zalika ya bayyana farin cikinsa da gagarumar nasarar da Buhari ya samu ta bangaren samar da manyan ayyuka da ababen more rayuwa a dukkanin sassan kasar nan.

“An samu cigaba a sha’anin noma, kuma ya kamata mu cigaba a kan wannan turba, an samu nasara a yaki da ta’addanci, ga kuma kyakkyawar alaka da aka samu tsakanin bangaren majalisa da kuma bangare zartarwa. Idan aka duba da kyau shekarar 2019 ta yi ma shugaban kasa kyau, kuma abin a yaba masa ne.” Inji shi.

Game da rade radin rikicinsa da gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje kuwa, Jibrin yace: “Ba gaskiya bane, jita jita ne kawai, muna aiki tare da shi, kuma ina sa ran zan samu nasara a zaben da za’a sake gudanawa, alakata da Ganduje na nan yadda aka santa, tamkar Uba da Dansa.”

Idan za’a tuna wata kotun daukaka kara ne ta fatattaki Jibrin daga majalisa, inda ta umarci hukumar INEC ta shirya wani sabon zabe, daga bisani INEC ta sanya ranar 25 ga watan Janairu domin sake gwabzawa tsakanin masu neman kujerar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel