Kuma dai: Gobara ta tashi a kasuwar Jos, ta lakume shaguna 14

Kuma dai: Gobara ta tashi a kasuwar Jos, ta lakume shaguna 14

Wani bangare na kasuwar Katako da ke Karamar hukumar Jos ta arewa na jihar Plateau ya kama da wuta. An tattaro cewa shaguna 14 ne suka kone kurmus.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa dukkanin bangaren da abun ya shafa ya kone kurmus.

Lawal Kamal, shugaban Body B, wanda ya tabbatar da lamarin ya bayyana cewa lamarin ya fara ne da misalin karfe 3:30 na tsakar dare sannan ya lakume bangaren baki daya kafin zuwan masu kashe gobarar. Ya ce na’urar lantarki ne ya haddasa gobarar.

Wannan ba shine karo na farko da kasuwar ke fuskantar gobarar ba.

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa wasu bangarori na kasuwar Kara hanyar babbar titin Lagas- Ibadan a ranar Talata, 31 ga watan Disamba, sun kama da wuta.

KU KARANTA KUMA: Tsohon IGP Idris ya karyata ikirarin shiga siyasar Neja

Koda dai annobar ta lalata ababen hawa da shaguna da dama a shahararriyar kasuwar dabbobin, babu wani jawabin mahukunta kan abunda ya haddasa lamari ko kuma yawan asarar da aka yi zuwa yanzu, jaridar The Nation ta ruwaito.

Idon shaida da yan jarida sun rahoto cewa lamarin ya haddasa cunkoso sosai a hanyar babban titin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel