Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun kashe mutum 1, sun sace uwa da danta

Yan bindiga sun kai hari Katsina, sun kashe mutum 1, sun sace uwa da danta

An sake kwatawa, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da wani hari a karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina, inda suka halaka mutum daya, tare da yin awon gaba da wata Mata da Danta daya.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Gambo Isah ne ya tabbatar da haka, inda yace baya ga kashe mutum guda da sace matar da danta, yan bindigan sun yi awon gaba da wani mutumi na daban.

KU KARANTA: Ganduje zai kashe naira biliyan 2.5 don gina manyan asibitoci a sabbin masarautu

Gambo yace da misalin karfe 8 na daren Lahadi ne yan bindigan suka kutsa kai cikin garin Jibia a kan babura inda suka dinga harbin mai kan uwa da wabi, wanda dalilin haka suka sami wani matashi Ibrahim Usman dan shekara 20, nan take ya fadi matacce.

“Kai tsaye yan bindigan suka zarce zuwa gidan Tasiu Waliyi inda suka dauke matarsa da Danta da kuma wani mutumi a gidan mai suna Abu Abu, suka shige dasu cikin daji. Amma tuni rundunar ta aika jami’an Operation Puff Adder da yansandan SARS zuwa cikin dajin da nufin kubutar dasu.” Inji shi.

Wata majiya ta tabbatar da cewa yan bindigan da adadinsu ya kai mutum 10 sun shiga garin ne sanye da abin kariyan fuska, dauke kuma da muggan makamai, inda suka zarce gidan Tasiu Waliyi, suka amshe wayoyin salulan makwabtansa, sa’annan suka kwantar da duk wanda ke wajen.

Haka zalika rahotanni sun tabbatar da yan bindigan sun kwashe makudan kudade da sauran kayayyaki masu muhimmanci daga gidan Waliyi.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai wani mummunan hari a kauyuka guda hudu dake cikin karamar hukumar Dutsanman jahar Katsina, inda suka sace mutane uku tare da awon gaba da shanu da dama.

Yan bindigan sun yi awon gaba da mutane biyu a kauyen Maitsani da suka hada da Sale Rahama da Bilkisu Sunusi, sa’annan suka dauke Alhaji Bello Suke a kauyen Darawa, yayin da a kauyen Madagu kuwa suka tattara shanu 60 da tumaki 40, haka zalika sun kwashe dabbobi da dama daga kauyen Gefen Kubewa, duk a cikin karamar hukumar Dutsanma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel