Motar yaki ta Sojoji ta babbake a garin Damaturu

Motar yaki ta Sojoji ta babbake a garin Damaturu

Wata tankar yaki ta sojoji a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, ta kama da wuta a Damaturu, jihar Yobe inda hakan ya yi sanadiyar tashe-tashen ababen fashewa da dama daga motar.

Fashewar abubuwan ya jefa garin baki daya cikin tashin hankali yayinda mazauna yankin suka bazama domin neman kariya.

Kakakin rundunar Operation Lafiya Dole sashi na II, Kyaftin Njoka Irabor ya tabbatar lamarin.

Kyaftin Irabor ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki amma ya ce lamarin bashi da alaka da kowani hari a yankin. Ya yi kira ga mutane da su cigaba da gudanar da harkokin gabansu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an zuba ma’aikatan kashe gobara omin kashe wutar.

A cewar idon shaida lamarin ya afku ne a tsallaken makatar Poly na tarayya da ke Damaturu yayinda sojojin ke a hanyarsu na komawa sansaninsu daga filin wasa na August 27 Damturu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari na cikin ganawa mai muhimmanci da shugabannin tsaro (hotuna)

A wani labari na daban, mun ji cewa Biyo bayan kisan wasu Kiristoci 11 da aka yi a ranar Kirsimeti, da kuma muzgunawa Kiristoci a wasu yankunan Najeriya, kungiyar attawan Kiristocin kasar (NCEF), ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar za a rike kan habbakan ayyuka da ta’asar yan taddan ISWAP, Boko Haram da kuma makiyaya a kasar.

Hakan na zuwa ne yayinda cigaba da kasancewar Leah Sharibu a hannun yan ta’addan Boko Haram sama da shekara biyu ke kara janyo hankulan mutane a gida da waje, inda suke kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da ganin cewa matashiyar yarinyar bata shiga sabon shekara a hannun yan ta’addan ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel