Bincike: Cin zogale ga mata masu ciki na da matukar illa ga jariran cikinsu

Bincike: Cin zogale ga mata masu ciki na da matukar illa ga jariran cikinsu

- Ba bakon abu bane idan aka sanar da mai karatu cewa zogale na maganin manyan cututtuka masu yawa

- Sai dai kuma masu bincike sun gano illar ganyen zogale, ‘ya’yan shi da man shi ga mace mai juna biyu

- Yana sa mace ta haifo da mara wasu sassa na jiki ko kuma yaro mara karfin kasusuwan jiki

Sanannen abu ne cewa zogale ganye ne dake dauke da sinadarai daka samar wa mai ci lafiya da kuma kare shi daga kamuwa da cututtuka. Hakan kuwa bai hana binciko wasu illolin da ke tattare da cin shi ba musamman ga mata masu juna biyu.

Ganyen zogale na taimaka wa wajen kawar da hawan jini, cututtukan dake kama zuciya, ciwon suga, cutar daji, inganta fatar mutum da dai sauransu.

Sai dai kash! Duka amfanin da zogale ke da shi a jiki, ma’abota bincike daga jami’ar Ibadan sun yi kira ga mata masu juna biyu da su guji cin ganyen zogale, ‘ya’yan zogale da man zogale domin yana yi wa dan dake ciki illa.

Farfesa Adefolarin Malomo, Foluso Atiba da Dr Innocent Imosemi ne suka gano haka a binciken da suka gudanar a jikin wasu beraye 20 da ke dauke da ciki.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 10 na yadda ake amfani da ganyen mangwaro wajen magani

Sakamakon binciken ya nuna cewa ganyen Zogale na yi wa kwakwalwa, jijiyoyi da kasusuwan jaririn dake ciki illa matuka tun kafin ya zo duniya.

Malamo ya ce alamun illolin da Zogale ke yi wa jarirai sun hada da haifo dan da bashi da kafafuwa ko kunne ko baki ko cibiya sannan kuma da kasusuwa marasa karfi da dai sauran su.

Likitocin sun yi kira ga mata masu ciki da su hakura da cin ganyen Zogale a duk lokacin da suke dauke da ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel