Tirkashi: Ango yace allan fur ya fasa auren amaryarshi bayan ya gano sun kai shi wajen bokaye da 'yan bori ita da mahaifiyarta

Tirkashi: Ango yace allan fur ya fasa auren amaryarshi bayan ya gano sun kai shi wajen bokaye da 'yan bori ita da mahaifiyarta

- Bayan kammala duk shirye-shiryen aure a mako mai zuwa, ango ya ce ya fasa

- Angon ya gano cewa an mika hotunan shi da sunan shi ga ‘yan bori da bokaye don mallaka

- Asirin amarya ya tonu ne bayan da ango ya ci karo da hirar amarya da mahaifiyarta a Whatsapp

Bayan kammala duk shirye-shiryen bikin da za a yi a makon da ke zuwa, ango ya sanar da fasawarsa. Wannan lamarin kuwa ya jawo tashin hankula daga dangi, abokai da ‘yan uwa.

Daga bisani angon ya bayyana cewa, ya fasa ne bayan da ya bankado cewa sirikarshi wato mahaifiyar amarya ta garzaya wajen ‘yan bori da bokaye da hotunanshi da sunan shi don neman mallaka.

Kamar yadda wani ma’abocin amfani da kafar sada zumunta ta tuwita mai suna Nnamdianekwe ya bayyana, angon mazaunin kasar ketare ne. Kuma ya fasa auren ne sakamakon ganowa da yayi an mika sunanshi gaban ‘yan bori da bokaye.

Kamar yadda Nnamdianekwe ya bayyana, angon ya fasa auren ne bayan da ya ga hirar kafar sada zumuntar zamani ta Whatsapp tsakanin mahaifiyar budurwarshi da budurwar.

KU KARANTA: Hotuna: Dan sanda ya yiwa matarsa dukan kawo wuka kan N500 a Kaduna

Mahaifiyar ta sanar da budurwar tashi cewa ta mika sunanshi da hotunanshi ga ‘yan bori da bokaye.

Ya wallafa, “Wani auren da za a yi a mako mai zuwa ya fasu. Hakan ya faru ne bayan ango ya ci karo da hirar amarya da mahaifiyarta. Mahaifiyar ta bayyana cewa ta mika hotunan saurayin da sunanshi don su mallakeshi.

“Wannan labarin na cike da abun mamaki. Ya yawaita a cikin kwanakin nan. Matsalar ita ce, baka san ko kaima ana mallakeka ba. Lamarin na saka rashin yadda tsakanin mutane.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel