A raba kowa ya samu: El-Rufai ya baiwa Kaakakin majalisar Kaduna rikon jahar Kaduna

A raba kowa ya samu: El-Rufai ya baiwa Kaakakin majalisar Kaduna rikon jahar Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mika mulkin jahar Kaduna ga Kaakakin majalisar dokokin jahar Kaduna, Aminu Abdullahi Shagali, a matakin rikon kwarya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hadimin Shagali, Muhammad Mustapha Angry Ustaz ne ya bayyana haka a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook a ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, inda yace Kaakakin majalisa Shagali ne zai cigaba da juya akalar jahar Kaduna har zuwa lokacin da gwamnan zai dawo.

KU KARANTA: Sulhu alheri ne: Kalli manyan mutane 10 da zasu shiga tsakanin Ganduje da Sarki Sunusi

Daga karshe sanarwar ta yi fatan Allah Ya taimaki sabon gwamnan jahar Kaduna, Ya kuma shiryar da shi tare da kara ma basira wajen gudanar da al’amuran gwamnatin yadda ya kamata.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne muka kawo muku rahoton yadda Aminu Shagali ya gwangwaje tsofaffin Malamansa na FGC Daura da kyautar motocin kece raini guda 7 a matsayin sakayyar koyarwar da suka yi masa.

Shagali ya kammala karatun sakandari a kwalejin gwamnatin tarayya dake Daura ne a shekarar 1995, kuma ya yi ma malaman kabakin alherin ne a ranar bikin cikar kwalejin shekaru 30 da kafuwa, bikin daya samu halartar manyan mutane da suka yi karatu a makarantar daga sassa daban daban na Najeriya.

A hannu guda kuma, gwamnatin jahar Kaduna ta dauki nauyin daliban jahar guda bakwai domin yin karatu a jami’o’in kasar Sudan, daliban sun tafi karatun ne a ranar 9 ga watan Disamba, wanda ya kawo yawon daliban jahar Kaduna dake karatu a Sudan zuwa 14.

Hukumar bada tallafin karatu na jahar tare da hadin gwiwar gidauniyar attajiri Alhaji Muhammadu Indimi ne suka dauki nauyin daliban, inda gidauniyar ta zabo jami’ar da za’a kai daliban, sa’annan ta biya musu kudin makaranta tare da wurin zamansu, yayin da hukumar ta biya musu kudin tafiya da kuma kudin wata wata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel