Amfanin ridi 13 a jikin dan adam da ba kowane ya sani ba

Amfanin ridi 13 a jikin dan adam da ba kowane ya sani ba

- Mutane na amfani da Ridi wajen yin abubuwa da dama

- Ana amfani da Ridi wajen yin abinci da sauransu

- Ridi na da amfani da yawa a jikin dan Adam don yana yaye wasu cutuka

Mutane na amfani da Ridi wajen yin abubuwa da yawa ballantana wajen yin abinci da sauran su.

Mutane da dama na da masaniya game da ridi sai dai yadda suke amfani da ita ne ya banbanta.

Ana amfani da ridi wajen ci haka kawai, da suga ko kuma da gishiri. Wasu kan hada shi don maganin bakon dauro ko kyanda a yara da sauransu.

Likitoci sun yi kira ga mutane da su rika cin ridi don amfanin da yake da shi a jikin dan Adam.

KU KARANTA: Rahama Sadau: Yadda za'a kawo gyara a harkar fina-finan Hausa

Ga wasu amfanin Ridi:

1. Ridi na rage cutar siga wato ‘Diabetes’.

2. Yana taimaka wa masu fama da ciwon ido.

3. Ridi na taimakawa wajen nika abinci a cikin mutum.

4. Yana rage kiba a jiki

5. Yana kuma kawar da cututtukan dake kama zuciya.

6. Ridi na maganin Asma.

7. Ridi na dauke da sinadarin Iron dake taimakawa wajen kawar da cututtukan dake kama jini.

8. Yana dauke da sinadarin Folic Acid dake taimakawa mata masu ciki da dan dake cikin su.

9. Ridi na karfafa karfin kashin dan Adam.

10. Yana kawar da cututtukan dake kama fata kamar su kuraje, kuma yana hana tsufa da wuri.

11. Ridi na inganta hantar mutum.

12. Yana taimakawa maza da mata wajen saduwa.

13. Yana maganin bakondauro ko kyanda ga yara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel