Kwankwasiyya: Ahmed Lawan ya baiwa jarumi Mustapha Nabruska mukami

Kwankwasiyya: Ahmed Lawan ya baiwa jarumi Mustapha Nabruska mukami

- Sashin labarai na kamfanin haska fina-finan Hausa na Northflix, ya bayyana cewa Mustapha Nabraska ya samu mukami a ofishin Ahmed Lawan

- A ranar Larabar da ta gabata ne aka bayyana cewa, shugaban majalisar dattijai ya ba jarumin mukamin mai bashi shawara ta musamman

- Kamfanin ya tabbatar da cewa, an ba shi wannan mukamin ne saboda cigaban al'umma tare da habaka ta

Sashin labarai na kamfanin haska fina-finan Hausa na Northflix ya bayyana cewa, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya ba wa jarumin fina-finan Hausa Mustapha Nabraska mukamin mai bashi shawar na musamman.

A ranar Larabar da ta gabata ne jarumin fina-finan barkwancin, ke bayyanawa a shafinsa na sada zumunta na Instagram inda yake shaidawa duniya wannan albishir.

DUBA WANNAN: Ganduje ya gwangwaje Sadiq Daba ta kyautar miliyan N1

Ya wallafa rubutu kamar haka: "Dukkan godiya ta tabbata ga Allah. Mun shiga aiki gadan-gadan a majalisa. Nayi nasara zama mai bada shawara na musamman na shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan."

Kamar yadda gidan rediyon Dabo FM ya ruwaito, ba a tabbatar da hakan ba don bata samu zantawa da jarumin.

Northflix ta ce: "Sanata Ahmed Lawan ya ba shi wannan mukamin na mai ba shi shawara ne kan harkokin ci gaban al'umma."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel