Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun Kirsimeti da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Laraba, 25 ga wata, da ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba 2019, da kuma ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, 2020, a matsayin ranakun hutun bikin Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a cikin sanarwa da sakataren ma'aikatar harkokin cikin gida, Barista Georgina Ehuriah, ya fitar ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba.

Da yake taya 'yan Najeriya da ke zaune a gida da ketare murnar zagayowar lokacin bikin Kirsimeti na wannan shekarar, Aregbesola ya bukaci mabiya addinin Kirista da su kasance masu koyi da biyayya ga koyarwar Yesu Almasihu a kan kaunar juna da zaman lafiya.

Kafin fitowar wannan sanarwa, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zartar wa ta tarayya (NEC) na ranar Alhamis a fadar shugaban kasa, Villa, dake Abuja.

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutun Kirsimeti da sabuwar shekara
Rauf Aregbesola; Ministan harkokin cikin gida
Asali: Depositphotos

Taron shine na karshe da NEC zata yi a cikin shekarar 2019. Osinbajo ya jagoranci taron ne a daidai lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tafi jihar Kano domin halartar taron yaye 'yan sanda a Wudil.

DUBA WANNAN: Sunaye: APC ta kafa kwamitin sulhu mai mutane 10 a karkashin Lawan

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa mataimakin shugaban kasa ne zai kasance jagoran taron.

Ana gudanar da taron NEC ne kowanne mako domin tattauna wa da kuma tsara aiyukan gwamnatin tarayya a kowanne mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel