Tirkashi: Shugaban kasar Zambiya ya yiwa jakadan Amurka korar kare bayan yayi magana kan Luwadi

Tirkashi: Shugaban kasar Zambiya ya yiwa jakadan Amurka korar kare bayan yayi magana kan Luwadi

- Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, ya bukaci jakadan kasar Amurka da ya tattara ya bar kasar

- Hakan ya biyo bayan rokon da jakadan yayi don a sassautawa wasu ‘yan luwadi da aka yankewa hukuncin kisa

- Shugaban kasar ya jaddada cewa, in har ta haka zai taimakawa kasar, toh basu bukatarsa a tare dasu

Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu, ya bukaci jakadan kasar Amurka da ya bar kasarsa a kan rokon gwamnatin da yayi ta duba, bayan da aka yankewa wasu ‘yan luwadi hukuncin kisa a kasar.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da Skynews a ranar Lahadi.

“Mun kai kokenmu ga gwamnatin kasar Amurka, kuma muna jiran martaninsu saboda bamu da bukatar ire-iren mutanen nan a tsakankaninmu. Muna da bukatar ya tafi.”

KU KARANTA: Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba

A watan da ya gabata ne, jakadan kasar Amurka, Daniel Foote, ya ce, ya firgita bayan da kotu ta yankewa wasu ‘yan luwadi hukuncin kisa. Ya yi kira ga gwamnatin da ta dubi dokar da ke ladabtar da wasu tsirarun kungiyoyi.

“Bamu bukatar neman jinsi. Idan kana kokarin taimakawa hakan, kana tunanin ta hakan zaka taimaka, toh ina tunanin bamu da bukatarku a tare damu, zaku iya barinmu cikin talaucinmu. A hakan zamu cigaba da fafutuka.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel