Da zafi zafi: Wani babban Sanatan jam'iyyar APC daga kudancin Najeriya ya rasu

Da zafi zafi: Wani babban Sanatan jam'iyyar APC daga kudancin Najeriya ya rasu

Wani rahoto da ya fito da dumi duminsa daga jaridar Premiu Times ya tabbatar da mutuwar Sanata mai wakiltar mazabar Imo ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Benjamin Uwajumogu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sanata Benjamin ya mutu ne da sanyin safiyar Laraba, 18 ga watan Disamba a babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da doguwar jinya a sanadiyyar wata cuta da ba’a bayyana ba.

KU KARANTA: Tuwo na mai na: Shugaba Buhari ya nada uwargidar minista Ngige mukamin babbar sakatariya

Da zafi zafi: Wani babban Sanata daga kudancin Najeriya ya rasu

Benjamin
Source: Facebook

Abokinsa, kuma takwaransa a majalisar dattawa, Sanata Elisha Abbo ne ya tabbatar da mutuwar Sanatan, inda yace: “Ina tabbatar muku da mutuwar abokina kuma dan uwana Ben Uwajumogu, wannan abin tausayi ne.

“Wannan tabbaci ne na cewa duniyar tamu tamkar kasuwa muke ci a cikinta, idan har ka shigo cikinta, dole ne ka koma, Ben ya ci kasuwa da kyau kuma ta tashi, don haka ya koma ya yi bayanin alkhairan da ya aikata a duniya.” Inji shi.

Sanata Benjamin ya lashe zabensa ne a karkashin inuwar jam’iyyar APC, inda a kwanakin baya aka garzaya da shi kasar Dubai domin duba lafiyarsa, amma daga bisani ya dawo Najeriya tare da alamun waraka a tare da shi, kamar yadda wani makusancinsa ya bayyana.

Haka zalika wani babban hadimin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa maigidansa bai sanar da mutuwar ba, amma tuni iyalan mamacin suka sanar da shi, kuma zai sanar da majalisar nan bada jimawa ba.

Sanata Ben Uwajumogu ya mutu yana da shekaru 51 a duniya, yana da mata da yara da sauran yan uwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel