Mutane 6 sun halaka yayin da kasa ta zurma dasu yayin da suke hakar ma’adanai a Jos

Mutane 6 sun halaka yayin da kasa ta zurma dasu yayin da suke hakar ma’adanai a Jos

Mutane shida ne suka gamu da ajlinsu yayin da kasa ta rufta a kansu a lokacin da suka tsaka a aikin hakar ma’adanan kasa a yankin Zawan cikin karamar hukumar Jos ta kudu a jahar Filato.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito dan majalisa mai wakiltar mazabar Jos ta kudu a majalisar dokokin jahar, Gwottson Fom ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN a ranar Laraba.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 3 yan gida daya a Katsina

Fom yace shekarun mamatan bai wuce tsakanin 20 zuwa 27 ba, kuma ya bayyana lamarin a matsayin mummunan hatsari abin takaici, sai dai yace tabbas masu hakar ma’adanan suna yi ne ba bisa ka’ida ba, amma rashin aikin yi ya kaisu ga shiga harkar.

“Mutane da dama na aikata haramtattun ayyuka domin su samu abin da zasu ciyar da kansu da iyalansu, duk da cewa yanzu ba lokacin fayyace mai lafi bane, amma rasa matasa shida majiya karfi a lokaci daya akwai zafi.

“Idan har lallai sai mutane sun shiga sana’ar hakar ma’adanan kasa, toh kamata ya yi su yi shi yadda ya kamata, su tabbata sun samu lasisin gudanar da sana’ar kamar yadda ya kamata.” Inji shi.

Wani shaidan gani da ido, Emmnuel Gyang ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da aka fara samun irin haka a garin, a cewarsa sama da mutane 50 ne suka cikin ramin hakar ma’adanan a lokacin da kasan ya rufta a kansu.

Daga karshe Gyang yace tuni sun gudanar da jana’izar mamatan guda 6, sa’annan sauran da suka samu rauni daban daban an garzaya dasu zuwa asibitin Our Lady Apostles Zawan domin samun kulawa.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da sabon farmaki a karamar hukumar Ganye na jahar Adamawa inda suka yi awon gaba da mata masu shayawar guda biyu da kuma kananan yara guda uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel