Matar mutum ajalinsa: Yadda wata Mata ta kashe mijinta da wuka da kwalba

Matar mutum ajalinsa: Yadda wata Mata ta kashe mijinta da wuka da kwalba

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Abakaliki na jahar Ebonyi ta bada umarnin garkame wata mata mai shekaru 40 a gidan gyara halinka biyo bayan tuhumar da ake mata na kashe mijinta.

Jaridar Punch ta ruwaito matar ta kashe mijinta, Nome Usulor ne ta hanyar caccaka masa wuka da kuma fasashshen kwalba a ranar 30 ga watan Nuwamba a unguwar Umoure-Oriuzor dake cikin karamar hukumar Ezza ta Arewa.

KU KARANTA: Yaba kyauta tukwici: Dalibi ya raba ma tsofaffin Malamansa motocin alfarma a Daura

Jami’in rundunar Yansandan jahar Ebobyi, ASP Mathias Eze ya gurfanar da ita gaban kotun inda ya shaida ma Alkalin kotun cewa laifin da ake tuhumar matar ya saba ma sashi na 319 (1) na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Ebonyi na shekarar 2004.

Sai dai lauyan wanda ake kara ya nemi a bayar da belinta, amma Alkalin kotun, Nenna Onuoha ta bayyana cewa ba za ta iya bayar belinta ba, duba da girman laifin da ake tuhumarta da aikatawa, sa’anan kuma kotun bata da hurumin sauraron karar.

Daga karshe bayan sauraron duka bangarorin biyu, kotun ta umarci a tasa keyar wanda ake tuhuma zuwa gudan gyara halinka, sa’annan ta mika takardar karar zuwa ga babban jami’I mai shigar da kara na jahar Ebonyi don daukan matakin daya kamata.

A wani labarin kuma, shugaban kungiyar daliban jami’ar jahar Filato, Ezekeil Lutei ya tabbatar da hari da wasu gungun yan bindiga suka kaddamar a jami’ar a ranar Talata, 17 ga watan Disamba, har ma suka yi ma wata daliba fyade.

Yan bindigan sun kai harin ne a jami’ar dake garin Bokkos kamar yadda shugaban daliban ya bayyana, ya kara da cewa sun yi ma dalibai da dama kwacen wayoyin salula da kudadensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel