Babbar magana: Tilas ka aureni ko kuma na saka mazakutarka ta daina aiki - Cewar wata budurwa ga saurayinta

Babbar magana: Tilas ka aureni ko kuma na saka mazakutarka ta daina aiki - Cewar wata budurwa ga saurayinta

- Wani mutumi mai shekaru 38 dan asalin kasar Afirka ta Kudu ya shiga tashin hankali bayan rabuwa da budurwarshi

- Bayan da yayi sabuwar budurwa, sai kwanciya da ita ya gagara don kuwa mazakutarshi ta dena aiki

- Lindiwe ta bayyana cewa mazakutarshi mallakinta ce kuma ta je boka ya rufe mata ne, zai fi mishi idan ya aureta

Wani mutumi da ya rabu da budurwarshi da suka yi shekaru 7 suna soyayya ya shiga halin tashin hankali. An bashi sharudda biyu tsaurara; ko dai ya koma su sasanta ko kuma mazakutarshi ta mutu.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito yadda wata budurwa ta yi amfani da sihiri inda ta rufe mazakutar saurayinta bayan sun rabu.

Nicholas Mofokeng mai shekaru 38 dan asalin yankin Holomisa ne da ke Ekurhuleni a kasar Afirka ta Kudu. Ya ce shi da budurwarshi masoyan juna ne na hakika da farko, don har alkawarin aurenta ya yi.

Sun fara zama tare ne bayan da suka shekara uku suna soyayya. Amma Nicholas ya yi ikirarin cewa Lindiwe Zungu mai shekaru 33 ta fara bayyana munanan halayenta.

"Ta fara juya ni. Ta koma mahaifiyata a maimakon masoyiyata," ya ce.

Ya ce, a lokacin da aka warware soyayyar, ta fusata matuka.

KU KARANTA: Kwamacala: Uba ya auri 'yar cikinsa bayan sun shafe shekaru suna soyayya

"Ta ce zata je wajen mashahurin boka don rufe mazakuta ta. A tunani na wasa take yi har sai lokacin da nazo kwanciya da sabuwar budurwata."

Likitoci sun ce mishi akwai yuwuwar gajiya ce ta hana shi iya kwanciya da mace. Amma a lokacin da ya sake kokarin kwanciya da mace, mazakutar ta ki aiki.

"Na je wajen wani boka wanda ya sanar dani cewa an rufe mazakutata ne. A lokacin da na kira ta, sai ta sheke da dariya kuma ta sanar dani sai dai in aureta ko kuma ba zan taba iya jima'i ba har karshen rayuwata."

Lindiwe ta sanar da jaridar Daily sun cewa: "Ya bata min lokaci. Na so shi kuma ba zan barshi ya je ko ina ba. Na yi tsufan da ba zan fara sabuwar soyayya ba."

Lindiwe ta ce, mazakutarshi mallakinta ce ita kadai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel