Sulhu alheri ne: Abdulaziz Yari da Kabiru Mafara sun kama hanyar dinke barakar APC a Zamfara

Sulhu alheri ne: Abdulaziz Yari da Kabiru Mafara sun kama hanyar dinke barakar APC a Zamfara

Tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Yari da Sanata Kabiru Marafa sun dauki gabaran daukan matakan dinke barakar dake tsakaninsu a siyasance, tare da daidaita siyasar jam’iyyar APC a jahar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa mai magana da yawun jam’iyyar APC a jahar, Shehu Isah ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Gusau a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Sanatoci sun yi tutsu ga takwarorinsu dake kokarin tsige shugaban majalisar dattawa

Kaakakin na APC, yace wadanda za’a yi sulhun da su, su ne jiga jigan yan siyasan da suka ja daga da Abdulaziz Yari a yayin zaben 2019, wadanda ake kira G8 da suka hada da; Sanata Kabiru Marafa, Dauda Lawal, Ibrahim Wakkala, Mahmud Shinkafi, Aminu Sani Jaji da sauransu.

Malam Isah yace guda daga cikin yan siyasan G8, Aminu Sani-Jaji ne ya gana da Yari a gidansa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata, inda suka tattauna a kan batutuwan da suka shafi dawo da martabar APC a jahar.

“Daga Jaji har Yari, dukkaninsu sun amince da kawar da banbance banbancen dake tsakaninsu domin ciyar da jam’iyyar APC gaba.” Inji mai magana da yawun APC a jahar Zamfara.

Shi ma shugaban jam’iyyar reshen jahar, Lawal Liman ya bayyana matakin sulhun a matsayin abin da ya kamata jam’iyyar ta yi, ko ba komai za ta samu nasara idan aka samu hadin kai, sa’annan ya kara da cewa suna fatan janyo dukkanin yayan G8.

A wani labarin kuma, majalisar dattawan Najeriya ta yi fatali da bukatar wasu yan tsiraru daga cikinsu na tsige shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan daga mukaminsa ta hanyar kada kuri’un amincewa, inji rahoton.

A ranar Talata, 10 ga watan Disamba ne wata takarda ta bayyana a gaban majalisar dake dauke da sunayen Sanatoci guda 36 wadanda ke neman ganin an kada kuri’un amincewa ga Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel