'Wannan kuma matsalarku ce ta cikin gida' - An mayar wa da Aisha martani a Tuwita

'Wannan kuma matsalarku ce ta cikin gida' - An mayar wa da Aisha martani a Tuwita

Cacar baki da muhawara ta barke a dandalin sada zumunta a tsakanin 'yan Najeriya biyo bayan kalaman Aisha Buhari a kan cewa Mamman Daura ya hada kai da Malam Garba Shehu domin wofantar da ita a matsayinta na uwargidan shugaban kasa.

A wani jawabi da ta fitar ranar Laraba, Aisha Buhari ta zargi Garba Shehu da rashin girmama ofishinta bisa umarnin Mamman Daura, dan uwan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Kamar yadda aka yi tsammani, 'yan Najeriya sun fara mayar wa Aisha Buhari martani a kalaman da ta yi, wadanda suka fito da barakar da aka dade ana zargin akwai a tsakanin uwargidan Buhari da wasu na hannun damunsa.

A yayin da wasu 'yan Najeriya ke zargin cewa Aisha Buhari na kokarin dauke hankalinsu ne kawai daga abubuwan da ke faruwa a kasa, wasu kuma rokonta suka yi da ta daina damun 'yan Najeriya da matsalarsu ta cikin gida da bata da nasaba da cigaban kasa ko jama'a.

'Wannan kuma matsalarku ce ta cikin gida' - An mayar wa da Aisha martani a Tuwita
Aisha Buhari
Asali: Depositphotos

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa uwargidar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, ta saki bama-baman kalamai a kan mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu.

Aisha ta bayyana cewa Garba Shehu, maimakon maida hankali wajen biyayya da kare shugaban kasa wajen al'umma, ya maida hankali wajen biyayya ga wasu yan tsiraru da aka fi sani da miyagun fadar shugaban kasa.

Ta zargi Garba Shehu da kullawa iyalan shugaba Buhari sharruruka tare da yi mata zagon kasa iri-iri wanda ya kai ga yiwa yaranta sharri.

DUBA WANNAN: Garba Shehu ya mika 'kambun' gwarzon shekara ga Dino Melaye

Aisha ta labarta cewa Garba Shehu ya yi tsayin daka domin ganin cewa an ci mutuncinta ta hanyar sallamar hadimanta kafin ta farga ta dakile hakan. Ta ce lallai Garba Shehu ya koma biyayya ga Mamman Daura maimakon shugaba Buhari.

Aisha tace: "Cigaban Najeriya na jingine da aiwatar da ayyukan ma'aikatan gwamnatin kamar yadda aka umurcesu, saboda su zama abin koyi ga al'umma."

"Ba abu mai kyau bane a ce ma'aikata su ajiye ayyukansu kuma su dauke hankalinsu. A matsayinsa na mai magana da yawun shugaban kasa, ai babban aikinsa shine kare mutuncin shugaban kasa da kuma tallata irin ayyukan kwarai da yakeyi aiwatarwa."

"Amma maimakon yin hakan, ya dauke biyayyarsa daga shugaban kasa zuwa ga wasu da basu da wani ruwa da tsaki kan yarjejeniyar da shugaban kasa yai da yan Najeriya a ranar 29 ga Mayun shekarun 2015 da 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel