Son kowa kin wanda ya rasa; Sarauniya Zozibini Tunzi a cikin hotuna

Son kowa kin wanda ya rasa; Sarauniya Zozibini Tunzi a cikin hotuna

- Kwanan nan ne aka zabi Zozibini Tunzi a matsayin Sarauniyar kyau

- Legit.ng ta tsakuro maku wasu daga cikin kyawawan hotuan Tunzi

- Mun dauko hotunan ne daga shafukan sada zumuntar Sarauniyar

Son kowa kin wanda ya rasa; Sarauniya Zozibini Tunzi a cikin hotuna
Sarauniya Zozibini Tunzi a cikin hotuna
Asali: UGC

Legit.ng ta kawo maku wasu daga cikin mafi kyawun hotunan Zozibini Tunzi, wanda aka zaba a matsayin Sarauniyar kyau a Garin Atlanta da ke Amurka.

Kafin yanzu Zozibini Tunzi ce Sarauniyar kyau ta kasar Afrika. A gasar Duniya na wannan shekara, ta doke kyawawan mata 90 daga sauran kasashe.

Babu tantama, Duniya ta sallama cewa Zozibini Tunzi kyakkyawa ce ta kin-karawa. Bugu da kari, Tunzi doguwar Budurwace mai shekaru 26 da haihuwa.

A farkon watan Agustan nan Tunzi ta zama Sarauniyar kyau ta kasar Afrika ta Kudu. Bayan watanni hudu cir, sai kuma ta mamaye Duniya, ta zo ta daya.

Zozibini Tunzi ce ‘Yar kasar Afrika ta Kudu ta uku da ta lashe wannan gasa. Bayan haka, ita ce Bakar farko da ta samu wannan kyauta a cikin sheakaru takwas.

Wani abin burgewa shi ne, wannan kyakkyawar Baiwar Allah ta yi karatun Digiri a shararriyar Jami’ar fasahar nan ta kasar Afrika ta Kudu ta Cape Peninsula.

Sauran wadanda su ka takewa Sarauniyar baya a gasar bana su ne Madison Anderson ta kasar Puerto Rica da ke zama a Amurka, ai kuma wata Sofia Aragon.

Ga dai karin wasu hotunan nan, abin ba a cewa komai:

Son kowa kin wanda ya rasa; Sarauniya Zozibini Tunzi a cikin hotuna
Sarauniya Zozibini Tunzi lokacin da ta lashe gasar gida
Asali: UGC

Son kowa kin wanda ya rasa; Sarauniya Zozibini Tunzi a cikin hotuna
Sarauniyar kyau ta kasar Afrika ta Kudu Zozibini Tunzi
Asali: UGC

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel