Kada ka gurbata tarihin sama da shekaru 1000 - Dattijan Kano sun gargadi Ganduje

Kada ka gurbata tarihin sama da shekaru 1000 - Dattijan Kano sun gargadi Ganduje

Dattawan jihar Kano karkashin kungiyar hadin kan Kano, ta yi kira ga Gwamna Abdullahi Umar ganduje da ya janye dokar kirkirar karin masarautu a jihar.

A takardar da aka fitar kuma Alhaji Bashir Tofa yasa hannu a ranar Lahadi, tare da wasu dattawa goma kuma suka mika ga manema labarai, dattawan sun nuna fushinsu a kan yunkurin gurbata tarihin masarautar na sama da shekaru 1000.

Idan zamu tuna, majalisar jihar Kano ta amince da bukatar karin kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar a ranar 5 ga watan Disamba. A ranar Alhamis din ne kuma Abdullahi Ganduje yasa hannu a sabuwar dokar.

Duk da wannan ne karo na biyu da Gwamnan ya mika wannan bukatar ga majalisar, an fara sa hannu a kanta ne a watan Mayu 2019. Amma babbar kotun jihar Kano din ta shafe dokar a ranar 21 ga watan Nuwamba karkashin jagorancin mai shari'a Jastis Usman Na'Abba.

Takardar ta ce, "Kungiyar hadin kan jihar Kano ba kungiyar siyasa bace ko kuma mai goyon bayan wani mutum ba. Kungiya ce da ke bin doka kuma masu mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaban jihar Kano.

"A don haka ne, muke nuna damuwarmu a kan yadda Gwamna Ganduje ya jajirce don tarwatsa masarautar jihar Kano. Wannan kuma kokari ne wanda kakanninmu suka yi na karni aru-aru," in ji takardar.

DUBA WANNAN: Sarki Sanusi ya aike wa gwamnatin tarayya sako

"Babu shakka masarautar Kano ta kasance tun da dadewa wani jigo na gyara tarbiya da tattalin arziki na jihar Kano din da Najeriya baki daya. Amma kuma yunkurin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje saboda wani ra'ayin kansa, zai iya tarwatsa kokarin kakanninmu."

Takardar ta koka da cewa, wannan yunkurin na Gwamna Ganduje kawai kokari ne na siyasantar da karfin masarautar a Najeriya, tare da yin watsi da kokarin mutane da dama.

"Yan Najeriya masu yawa a fadin kasar nan sun yi bayani tare da bayyana illolin abinda Gwamnan Kano din yake yunkurin yi ga masarautar. Domin kuwa tana daga cikin daular musulunci wacce ke karkashin jihar Kano."

"An ja hankalin gwamnan ba sau daya ba a kan ya duba dalilai kafin ya rarrabe masarautar Kano din saboda wani kudiri nashi na siyasa. Amma kuma siyasa ta rufe mishi ido wajen ganin illar hakan. A takaice dai ya tashi tsaye wajen lalata abinda Sheikh Usman Dan Fodio ya gina, wanda masararutar Kano ta ke wakilta."

Takardar ta ce, saboda dalilan siyasa ne gwamnan ya ki duba maganganun da zantukan hikimar da ake rubuto mishi a wasika ko a kafafen yada labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel