Wata sabuwa: Maza masu aure da basa son komawa gida ga matayensu sune suke haddasa cunkoso - Hukumar tsaro

Wata sabuwa: Maza masu aure da basa son komawa gida ga matayensu sune suke haddasa cunkoso - Hukumar tsaro

- A kokarin shawo kan matsalar cunkoso da cushewar tituna tare da ababen hawa a kasar Ghana, hukumomin sun samo sabon shiri

- A bincikenssu, an gano cewa, mazan aure ne ke cushe titunan da yammaci saboda basu komawa gidajensu da wuri

- Jami’an ‘yan sandan kasar zasu dinga yawo a mota da kuma a kafa don sabawa duk namijin auren da aka kama ya tashi aiki bai tafi gida ba

A matsayin hanyar shawo kan cunkoson ababen hawa a titunan kasar Ghana, binciken jami’an ‘yan sandar kasar ya nuna cewa mazan aure ne ke cushe titunan kasar.

Kamar yadda hukumar kula da sufuri (MTTD) ta kasar Ghana ta sanar, cunkushewar titunan kasar na biyo baya ne yayin da mazan aure suka tashi aiki kuma basu son tafiya gidajensu.

A yayin zantawa da jaridar DailyViewGh, shugaban sashin bincike na MTTD, SP Alexander Obeng ya ce, shirin shawo kan cunkoson da ke addabar titunan kasar ya fito daga MTTD kuma an mikashi ga hukumar yankin don tabbatarwa.

“Mun yi binciken dalilin da yasa maza masu aure ke zama a Ofis ko a waje saboda cunkoson. Da yawa daga cikinsu na zuwa gida ba da wuri ba kawai don gujewa cunkoso a kan tituna.

KU KARANTA: Babbar magana: Allah yayi mini baki babu wanda ya isa ya hanani magana - Aisha Buhari

“A don haka ne, zamu kara yawan jami’an ‘yan sanda don sintiri a motoci da kuma kafa. Duk namijin aure da muka kama bai tafi gida ba, zai dandana kudarshi. Dole ne ku dinga komawa gida a kan lokaci don gudun samun matsaloli da matanku.

“Hakan kuma zai kawo raguwar masu amfani da titunan idan yammaci ya yi. A lokacin da yawan cunkoson ababen hawa ya ragu, za a iya samun kai kawo na ababen hawan haya kuma aiyukan tattalin arziki zasu karu a birane da garuruwan kasar nan,” ya tabbatar.

Accra na kokarin shawo kan matsalar kai kawo tare da cigaban cunkoso a titunan kasar. Akwai yuwuwar yawan mutanen da ke babban birnin Ghana din da suka kai miliyan 2.27 su ninka hakan zuwa 2035. Hakazalika yawan ababen hawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel