Buhari ya nada dan Arewa mukamin babban daraktan kudi na CBN

Buhari ya nada dan Arewa mukamin babban daraktan kudi na CBN

Babban bankin Najeriya ta sanar da nadin Ahmed Bello Umar a matsayin sabon daraktan kudi na babban bankin bankin CBN biyo bayan karewar wa’adin uwargida Priscillia Ekwueme Eleje a kan mukamin.

Ahmed ya gaji Priscillia ne sakamakon kaiwa wa’adin yin ritaya daga aikin gwamnati da ta yi, kuma sanarwar ta kara da cewa nadin Ahme ya fara ne daga ranar Alhamis, 5 ga watan Disambar 2019.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga 2,000 sun mika makamansu ga gwamnan Zamfara

Sanarwar wanda ta samu sa hannun daraktan watsa labaru na babban bankin Najeriya, Isaac Okorafor ta bayyana cewa Umar ya taba rike mukamin daraktan sashin cinikayya da canjin kudi na babban bankin.

An haifi Umar a ranar 10 ga watan Yuli na shekarar 1963, kuma ya fara aiki a babban bankin Najeriya a shekarar 1989, Umar ya yi karatun digiri a fannin sharia’a a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya zama cikakken lauya a shekarar 1987.

Haka zalika Umar ya yi karatun binciken kudi mai shaidar ‘Information system audit and control association ISACA’, a birnin Ilinois na kasar Amurka, haka zalika ya halarci kwasa kwasai da dama da suka bashi kwarewar rike wannan mukami.

Daga karshe sanarwar ta karkarewa da cewa Umar yana da mata, kuma yana da yara.

A wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zargi gwamnonin jahohin Najeriya da karkatar da kudaden da aka basu domin cigaban ilimi a jahohinsu.

Atiku ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake jawabi a majalisar dattawan Najeriya inda ya je domin bayar da gudunmuwarsa tare da goyon bayan yunkurin samar da jami’ar Modibbo Adama a jahar Adamawa da kuma jami’ar kimiyyar noma a garin Funtua.

Atiku ya yi kira ga majalisun dokokin Najeriya da su gudanar da gyare gyare a dokokin Najeriya ta yadda duk gwamnan jahar da aka kama ya karkatar da kudaden da aka tura musu domin cigaban ilimi ba zai sake samun wadannan kudi ba, sai dai a tura ma makarantun kai tsaye.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel