Dana sani keya ce: Matar da ta kashe makudan kudade domin ta zama namiji ta dawo tana so a mayar da ita mace ruwa a jallo

Dana sani keya ce: Matar da ta kashe makudan kudade domin ta zama namiji ta dawo tana so a mayar da ita mace ruwa a jallo

- Debbie Karema mai shekaru 61 ta sauya halittarta daga mace zuwa namiji amma tana da ta sani

- Ta aikata hakan ne yayin da take da shekaru 44 saboda yadda mahaifinta ya ci zarafinta lokacin tana matashiya

- Ta bayyana komawa jinsin da ba nata ba da babban kuskuren da ta tafka a rayuwarta

Debbie Karema mai shekaru 61 ce dake yankin Yemel Hempstead Hertfordshire, wacce take son komawa asalin siffarta bayan da ta koma namiji lokacin da take da shekaru 44 a duniya.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, ta yanke hukuncin komawa namiji ne saboda duniya ta karbeta kuma ta tsallake yadda ake banbanta yara mata a duniya.

Debbie ta bayyana yadda mahaifinta ya ci zarafinta lokacin da take matashiya.

A kokarin cika burinta, an yi mata aiki na mayar da ita cikakken namiji inda aka samar da mazakuta ta fatar cinyar hannunta.

Ta sauya sunanta zuwa Lee duk da cewa tana shan maganin samar da sinadarin 'testerone' na shekaru 17 don mayar da ita cikakken namiji.

"A zatona zan sauya zuwa wani mutum na daban ne. Zan bar wannan macen da nake tun farko, in koma namiji," in ji ta.

Amma kuma, tace tana jin kanta ne a matsayin mace da take daddaure a gangar jikin namiji, kari da cewa wannan babban kuskure ne da ta tafka.

KU KARANTA: Sun taru su uku sun kashe mahaifinsu saboda fyade da yake yi musu kullum

"Wannan kuskure ne da nake dana sanin aikatawa... Ta yaya zan koma Debbie din da nake?," ta tambaya.

Tace tana magana ne don ta hana wasu yin wannan mummunan kuskuren da ta tafka.

"Ya bayyana cewa, canza halitta babban kuskure ne. A lokacin kuwa da na gane kuskure ne, komai ya kammala," jaridar Daily Mail ta ruwaito.

A shekaru 61 da Debbie take dasu a duniya, ta fara komawa asalin halittarta ta mace.

Wannan na daya daga cikin abubuwan da ke faruwa da mutanen da ke canza jinsinsu.

James Caspian likita ne da ya samu ganawa da masu son komawa asalin jinsinsu. Ya ce sau da yawa wannan hukuncin na biyo baya ne idan suka gane hadurran da ke kunshe da zama mace.

"Wannan fannin sauyin jinsin na karkashin bincike ne a kowanne lokaci," in ji shi.

"Da yawansu suna samun munanan abubuwa na faruwa dasu ne a yayin da suke da jikin mata." Cewar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel