Attajiran Sarakunan gargajiya 5 da adadin kudin da suka mallaka

Attajiran Sarakunan gargajiya 5 da adadin kudin da suka mallaka

Duk da ana mulkin dimokradiyya ne a Najeriya, har yanzu sarautar gargajiya tana da daraja kuma sarakunan gargajiya na taka muhimmiyar rawa a harkokin mulki da jagoracin jama'a.

Sarakuna sun banbanta, haka ma darajarsu ta daya take ba.

Ga wasu manyan sarakunan gargajiya 5 a Najeriya da suka mallaki dukiya mai yawa da kuma kiayasin adadin kudin da suka mallaka.

5. Oba na Benin:

Oba Ewuare II na Benin, shine babban sarkin yanka a jihar Edo.

An nada shi a shekarar 2016, kuma shine sarki na 40 a jerin sarakunan masarautar Benin. Ya yi aiki a majalisar dinkin duniya daga shekarar 1981 zuwa 1982. Kazalika, ya kasance jakadan Najeriya a kasar Sweden, Angola da Italy.

Basaraken yana daya daga cikin manyan attajirai a Najeriya kuma ya mallaki manyan kadarori da wata motar alfarma kirar Rolls Royce Phantom 2016.

An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $60.

4. Sarkin Ife

Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi daya ne daga cikin manyan sarakunan kabilar Yoruba, shine babban sarkin masarautar Ile-Ife.

An nada shi a shekarar 2015, kuma yana daya daga cikin attajiran sarakunan gargajiya da ke Najeriya, sannan mai karfin iko a kasar Yoruba.

Ya mallaki kadarori da manyan motocin alfarma da suka hada da Rolls Royce da Bentley.

An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amur miliyan $700.

3. Sarkin Kano:

An nada Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano a shekarar 2014 bayan mutuwar tsohon sarki, marigayi Ado Bayero.

Sarki Sanusi II ya taba rike mukamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), kuma jaridar Forbes ta lissafa shi a cikin manyan mutane 100 a duniya.

An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurma miliyan $800.

2. Sultan na masarautar Sokoto:

An haifi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar a ranar 24 ga watan Agusta na shekarar 1956, kuma shine Sultan na 20 a masarautar Sokoto.

Sultan ne sarki mafi karfin iko a yankin arewacin Najeriya, kuma shine shugaban kwamitin koli na Musulunci a Najeriya.

Ya yi aikin soja kafin daga bisani a nada shi a matsayin Sultan a shekarar 2006.

An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $120 da kadarori da motocin alfarma da suka hada da Rolls Royce 2017.

1. Olugbo na Masarautar Ugbo:

Fredrick Obateru Akinaruntan shine sarkin masarautar Ugbo da ke karamar hukumar Ilaje a jihar Ondo.

Shine basarake mafi kudi a sarakunan gargajiya da ke Najeriya, sannan kuma na biyu a gaba daya nahiyar Afrika.

Sai dai, Basaraken, ba daga sarautar gargajiya ya samu kudinsa ba, dan kansuwar harkar man fetur ne. Ya mallaki wani kamfanin man fetur da makamashin Gas da ake kira da suna "Obat Oil".

An yi kiyasin cewa ya mallaki a kalla dalar Amurka miliyan $125.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel