Rikicin Yan-Uba: Dubun barawon daya sace kanwarsa yar shekara 6 a Katsina ta cika

Rikicin Yan-Uba: Dubun barawon daya sace kanwarsa yar shekara 6 a Katsina ta cika

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Katsina sun samu nasarar cafke wasni kasurgumin barawon mutane inda yake garkuwa dasu domin karbar kudin fansa bayan ya sace kanwarsa, karamar yarinya yar shekara 6.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a hedikwatar Yansandan jahar Katsina, inda yace sun kama barawon mai suna Ibrahim Kasim ne a ranar 28 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Abubuwa 5 game da dokar takaita amfani da kafafen sadarwar zamani

Rikicin Yan-Uba: Dubun barawon daya sace kanwarsa yar shekara 6 a Katsina ta cika
Kasim
Asali: Facebook

Kaakakin yace Ibrahim Kasim ya hada baki da wasu gungun masu garkuwa da mutane wajen sace kanwarsa da suke uba daya amma uwa kowa da tasa, Asiya Kasim mai shekaru 6, amma cikin ikon Allah Yansandan SARS suka ceto ta.

“Rundunar Yansandan SARS dake gudanar da aikin sintiri a karkashin jagorancin SP Andrew Alphouse ne suka kaddamar da wani samame har suka samu nasarar kama Ibrahim, kuma a yayin da ake gudanar da bincike ya amsa cewa ya hada baki da budurwarsa Murja yar jahar Zamfara wajen sace yarinyar.” Inji Isa.

Kaakakin Yansanan ya fallasa cewa Kasim ne ya baiwa gungun masu garkuwan lambar wayar mahaifinsu wanda suka yi amfani dashi wajen kiransa tare da bukatar ya biyasu naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa kafin su sako yarinya Asiya.

Daga karshe Gambo Isah yace rundunarsu na cigaba da gudanar da bincike tare da farautar sauran abokan ta’asan Ibrahim Kasim domin tabbatar da sun fuskanci hukuncin daya kamata, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito shi.

A wani labarin kuma, wani mummunan hatsarin kwale kwale ya rutsa da wasu yan mata guda shida a cikin wani ruwa dake karamar hukumar Suru ta jahar Kebbi, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban karamar hukumar, Alhaji Umaru Maigandi ya tabbatar da aukuwar hatsarin a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, inda yace jirgin ya kifa ne a lokacin da yake tafiya a cikin rafin Tindafi domin tsallakawa dasu a ranar Litinin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel