Za a bawa Kwamaret Muhammad Ali kason shi na kasafin kudin Najeriya, bayan ya nemi a bashi hakkinshi a wani sabon bidiyo

Za a bawa Kwamaret Muhammad Ali kason shi na kasafin kudin Najeriya, bayan ya nemi a bashi hakkinshi a wani sabon bidiyo

- A cikin makon nan ne wani faifan bidiyon wani bawan Allah daga jihar Jigawa ya yawaita a kafafen sada zumunta

- Shi dai bawan Allah na bukatar a bashi kasonshi ne a kasafin kudin shekarar 2020 na Najeriya

- Tuni dai hadimin shugaba Buhari, Bashir Ahmad ya yi alkawarin ba wa mutumin N50,000 don a kididdige hakan ne kasonshi a shekarar 2020

A cikin satin nan da muke ciki ne, faifan bidiyon wani bawan Allah dan jihar Jigawa ya bayyana. Bawan Allah na bukatar shugaba Buhari da ya bashi kasonshi a cikin kasafin kudin shekarar 2020.

Mutumin ya bayyana cewa bashi da bukatar duk aiyukan da shugaban kasar zai yi a cikin kasafin kudin.

A bangaren Bashir Ahmad, babban hadimin shugaba Buhari a kafafen sada zumunta, ya yi alkawarin biyan wannan bawan Allah kasonshi na kasafin kudin.

Dabo FM ta tabbatar da Bashir Ahmad na cewa, "A lissafin da nayi, idan za a raba tiriliyan 10 ga mutane miliyan 200, kowanne zai samu dubu hamsin ne."

Da yake bayyanawa a shafinshi na tuwita, Bashir Ahmad ya yi alkawarin ba wa bawan Allah N50,000.

KU KARANTA: Na Allah ba sa karewa: Dan acaba ya mayarwa da wani mutumi wayarshi iPhone 11 Pro da ya manta akan babur din shi

Sai dai yace zai bashi kudin ne domin samun nutsuwa da kuma kwarin gwiwar cigaba da sana’arshi cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Daga shafin na Twitter, Sani Ahmad Kaitafi da dan uwanshi, sun alkauranta bada tasu gudunmawar ta Naira 45,000.

Tini dai Bashir Ahmad, ya ayyana ya riski wanda zai yi masa iso domin sada Kwamaret da kudaden da suka alkauranta bashi.

Ga dai abinda Muhammad Ali ya ce a cikin bidiyon da ya saki makon da ya gabata:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel