Maryam Sanda: A Ranar Junairu 27, Alkalan kotu za su yanke hukuncin karshe

Maryam Sanda: A Ranar Junairu 27, Alkalan kotu za su yanke hukuncin karshe

Babban kotun tarayya da ke Unguwar Maitama a Abuja ya sa Ranar 27 ga Watan Junairun 2020, a matsayin ranar da za a saurari hukuncin da aka yanke a shari’ar Hajiya Maryam Sanda.

Ana zargin Maryam Sanda da laifin kashe Maigidanta, Bilyaminu Bello, wanda ‘Da ne a wajen tsohon shugaban jam’iyyar PDP da aka yi, Haliru Bello. Sanda ta karyata wannan babban zargi.

Har da Mahaifiyar wannan Baiwar Allah, Maimuna Aliyu da kuma ‘Danuwanta Aliyu Sanda, da ‘Yar aikin gidansu Sadiya Aminu ake kara a kotu da laifin sa hannu wajen wannan kisa.

Bilyaminu Bello ya mutu ne a Watan Nuwamban 2017 wanda ya sa ‘Yan sanda su ka shigar da kara su na zargin Matar da kashe shi da kuma hadin-kan sauran mutane uku da aka ambata.

Laifin da ake zargin wadannan mutane da shi, shi ne kokarin batar shaida ta hanyar goge wurin da ajalin Bilyaminu Bello ya auku. Daga baya kotu ya yi fatali da wannan zargi, ta kuma sake su.

KU KARANTA: Rashin ganin Maza ya na sa Mata ciwon tabin kwakwalwa

A zaman da aka yi jiya Ranar 2 ga Watan Disamban 2019, Lauyan ‘yan sanda, Fidelis Ogbobe, ya gabatar da duk tarin hujjojin da ke nuna cewa Maryam Sanda ce ta kashe Marigayi Bilya Bello.

Lauyan hukumar ya roki Alkali ya kama Sanda da laifi kuma ya daure ta. Sai dai Lauya Regina Okotie-Eboh, ta fadawa kotu cewa masu karar ba su iya gamsar da shari’a tuhumar da su ke yi ba.

Okotie-Ebor ta ce Likitocin da su ka duna Bello a asibiti ba su bada shaidar da ke nuna cewa kashe shi aka yi, kuma babu wani binciken asibiti da ya nuna haka, don haka ta nemi ayi fatali da karar.

An gurfanar da Sanda da sauran wadanda ake zargi a gaban kuliya a shekarar 2017. Bayan fiye da shekaru biyu da fara shari’a, Alkalai ya ce a Ranar 27 ga Junairun gobe, zai tsaida hukunci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel