Na Allah ba sa karewa: Dan acaba ya mayarwa da wani mutumi wayarshi iPhone 11 Pro da ya manta akan babur din shi

Na Allah ba sa karewa: Dan acaba ya mayarwa da wani mutumi wayarshi iPhone 11 Pro da ya manta akan babur din shi

- Wani dan Najeriya mai suna Abraham ya wallafa yadda wani dan achaba ya kai mishi wayarshi kirar Iphone 11 plus pro da ya yadda

- Abraham ya fito daga wani banki ne inda ya hau achaba don zuwa wani bankin a Ikoyi, amma sai ya yadda wayarshi

- Ya yi fatan sakayya mafificiya ga Simon tare da bayyana jin dadin wannan gaskiyar da ya nuna tare da halin nagarta

Wani dan Najeriya mai suna Abraham ya bada labarin yadda wani dan achaba ya dawo mishi da wayarshi kirar Iphone 11 bayan da ya yadda ta lokacin yana kan babur.

Mutumin ya wallafa yadda dan achaban mai suna Simon ya dinga binshi har zuwa lokacin da ya mika mishi wayar da ya yadda.

Abraham ya wallafa “Akwai mutane nagari a Najeriya. Na dau babur don zuwa wani banki a a Ikoyi. Wayata kirar Iphone 11 plus pro ta subuce ta fadi ina kan babur din. Wani dan achaba ya ganta, ya koma ya dauka sannan ya biyoni har bankin don bani kayata.

KU KARANTA: Babbar magana: Sai mun ga bayanka komin daren dadewa - Gargadin 'Yan Shi'a ga Shugaba Buhari

“Wannan ba yana nufin bani da kula bane, yana bayyana irin nagartattun mutanen da muke dasu ne a kasar nan. Nagode Simon. Ina fatan ka samu sakayya mafificiya fiye da wacce zan iya baka.”

Wayar Iphone 11 dai ta shigo ne a watanni biyu da suka gabata. Kadan daga cikin masu kudi ke iya mallakar wayar saboda irin tsadar da take da ita.

Don haka ne kuwa Simon ya cancanci jinjina saboda kyan hali da nagarta da ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel