Abin kunya: Gwmanatin Buhari ta bankado farfesoshi guda 100 na bogi a jami’o’in Najeriya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta bankado wasu manyan malaman jami’o’in Najeriya guda 100 masu darajar karatu ta Farfesa amma fa ta bogi, kamar yadda shugaban hukumar kula da jami’o’in Najeriya, NUC, ya bayyana.
Shugaban NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana hakane yayin wani taron shuwagabannin jami’o’in Najeriya daya gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda yace sun fallasa sunayen farfesoshin a shafin yanar gizo na hukumar, haka zalika sun aika sunayensu ga jami’o’in da suke koyarwa.
KU KARANTA: Gwamna Nasir El-Rufai ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 na jahar Kaduna
A yayin taron, Farfesa Rasheed ya bayyana cewa hukumarsa ta wallafa ka’idojin da ake bukatar kowacce jami’a ta cika kafin ta samu sahhalewar hukumar don gudanar da karatun digiri na farko, digiri na biyu da sauran matakan karatu da ake yi a jami’o’i.
Haka zalika ya umarci shuwagabannin jami’o’in da su umarci duk wani farfesa dake aiki a jami’arsu daya daura takardar shaidar karatunsa gaba daya a shafin yanar gizon hukumar NUC, inda yace ta haka ne hukumar zata kara yin tankade da rairaya don tantance sahihai daga cikinsu da kuma na bogi.
Farfesan ya kara da yin kira ga shuwagabannin jami’o’in dasu tabbata suna da cikakken alkalumman dalibansu da malamansu, sa’annan su dinga yin takatsantsan wajen rattafa hannu kan takardun shaidar kammala karatu da suke baiwa dalibai, inda yace shugaban hukumar NYSC ya yi masa korafin yadda wasu dalibai na amfani da takardun kammala karatu na bogi.
Bugu da kari ya ja kunnen shuwagabannin da su dakatar da al’adar nan da zaka ga malamin jami’a yana koyarwa a jami’o’I barkatai, inda yace doka ta bashi daman koyarwa a makarantu biyu ne kawai, haka zalika dole ne ba zai wuce awanni 8 yana koyarwa a kowanne rana ba.
Daga karshe Farfesa Rasheed ya nemi shuwagabannin dasu bada gudunmuwa wajen ganin an kawar da cin hanci da rashawa daya dabaibaye bangaren karatu a matakin jami’a, sa’annan ya basu kwarin gwiwar su kawo masa rahoton duk wani badakala da suka ji.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng