Yanzu-yanzu: Shugaban 'yan sandan Najeriya ya yi nasara a kotu

Yanzu-yanzu: Shugaban 'yan sandan Najeriya ya yi nasara a kotu

Babban kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, ta yi fatali da karar da ke kalubalantar shugaban 'yan sandan Najeriya na diban 'yan sanda 10,000 aiki a fadin kasar nan.

A yayin yanke hukunci a ranar Litinin, Jastis Inyang Ekwo ya ce, hukumar 'yan sandan karkashin jagorancin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya na da karfin ikon fitar da jerin sunayen mutanen da ta dauka aiki a hukumar.

Mai shari'a Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya yi watsi da karar da hukumar kula da aiyukan 'yan sanda (PSC), ta miko gabanta na kalubalantar ikon IGP da ya dauka sabbin jami'ai aiki a hukumar.

Alkalin ya bayyana yadda karar ta kasance mara makama. Ya kara da bayyana yadda PSC ta kasa bayyana yadda diban aikin ya take mata wani iko nata.

DUBA WANNAN: Zamfara: Kotu ta tsare tsohon kwamishinan Yari da aka gurfanar da laifin satar Shanu da garkuwa da mutane

"Na yanke hukuncin cewa, hukumar 'yan sanda karkashin jagorancin sifeta janar na 'yan sanda ne ke da alhakin diban ma'aikatan hukumar. A don haka ne na yi watsi da karar sakamakon rashin makama," Jastis Ekwo ya yanke.

Idan zamu tuna, an gano cewa hukumar kula da aiyukan 'yan sanda ta maka sifeta janar din hukumar 'yan sandan Najeriya a kotu a kan kalubalantar daukar ma'aikata 10,000 da ya yi, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta.

Kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1124/2019, an shigar da ita ne ta hannun lauyan masu koke, Kanu Agabi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel