San barka: Sarkin Kano Muhammadu Sanusi zai fitar da mahaddatan Al-Qur'ani karatu kasar waje

San barka: Sarkin Kano Muhammadu Sanusi zai fitar da mahaddatan Al-Qur'ani karatu kasar waje

- Mai martaba Sarki Sanusi II ya kai ziyara jami’ar Alkasimia don samarwa wasu mahaddatan jihar kano guraben karatu

- Sarkin ya bayyana taimakonsu da karatun zai yi tare da gudumawar da hakan zai taka wajen habaka karantar da alkur’ani

- A kwanakin baya, Sarkin ya jagoranci kulla alaka da zuba hannayen jari da kasar Sin zata yi a jihar Kano

Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyara jami’ar Alkasimia da ke garin Sharja a hadaddiyar daular Larabawa. Ya yi hakan ne don nemawa wasu mahaddatan alkur’ani na jihar Kano guraben karatu a makarantar.

A jawabin da Sarkin ya gabatar yayin ziyarar, ya bayyana cewa, jihar Kano na da makarantu da mahaddata alkur’ani. Wadannan mahaddatan zasu iya bayar da gagarumar gudummawa a bangaren alkur’ani da harshen larabci, idan suka samu gurbin karatu a wannan jami’ar.

Sarkin ya ce, “Akwai makarantu da mahadddata alkur’ani a Najeriya, musamman jihar Kano. Mahaddatan zasu iya bayar da gagarumar gudummawa a bangaren alkur’ani da harshen larabci idan suka samu gurbin karatu a wannan jami’ar.”

KU KARANTA: To fah: Babu yarinyar da iyayenta za su yadda ta shiga harkar fim da sanin su, ko nima sai da na samu matsala da su kafin na fara shiga - Hafsat Idris

Wata majiya daga fadar Sarkin ta ce, Sarki Sanusi ya samu ganawa da shugaban makarantar, Dakta Rashid Mohammed Salem da kuma sauran jami’anta. Sun ji dadin ziyararshi ba kadan ba.

Wannan dai ba shine karo na farko da Sarkin ya fara aiyukan habaka matasa ba da jihar Kano baki daya. Ko a kwanakin baya, Sarkin yya jagoranci kulla alakar kasuwanci da masu zuba hannayen jari na kasar Sin. Hakan kuwa zai bunkasa arzikin jihar Kano.

Hakazalika, mai martaba Sarki Sanusi ne jagoran samar da bankin musulunci na Ja’iz.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel