Aminai na gaske: Jerin mutane 7 dake tare da shugaba Buhari tun siyasar 2003

Aminai na gaske: Jerin mutane 7 dake tare da shugaba Buhari tun siyasar 2003

Sanannen lamari ne a zamantakewa cewa duk mutumin daya mori abokan arziki na amana lallai ba zai taba yin dana sanin zama dasu ba, sakamakon zasu kasance garkuwa da kariya a gareshi, kamar yadda shi ma zai kasanci garkuwa da kariya a garesu.

Ga duk wanda ya san tarihin siyasar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya san cewa daga shekarar 2003 ne Muhammadu Buhari ya fara taka kafa a farfajiyar siyasar Najeriya, inda ya tsaya takarar shugabancin Najeriya, daga cikin wadanda suka shawo kansa domin ya tsaya takarar akwai marigayi Wada Nasa.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya rattafa hannu a kan dokar haramta biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho

Aminai na gaske: Jerin mutane 7 dake tare da shugaba Buhari tun siyasar 2003

Mamman, Buhari, Darazau, Isa Funtua da Adamu
Source: Facebook

Legit.ng ta kawo muku jerin wasu mutane 7 wadanda shakikan shugaban kasa Muhammadu Buhari ne, kuma amintattu a wajensa, wadanda suka dade tare dashi, karanci tun daga shekarar 2003, yayin da wasu kuma tun suna kanana.

Manya manya daga cikin jerin wadannan mutane da suka tsaya tsayin daka a bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun hada da:

- Mamman Daura (Dan uwansa na jini)

- Samaila Isa Funtua (Surukinsa)

- Abba Kyari (Amininsa, kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa)

- Sarki Abba (Babban hadimin Buhari a kan harkar cikin gida)

- Adamu Adamu (Ministan ilimi)

- Mahmud Tukur (Abokinsa)

- Yau Darazau (Babban hadimin Buhari a kan ayyuka na musamman)

Wadannan shakikai na shugaban kasa Muhammadu Buhari suna taka rawa ta musamman a gwamnatinsa, har ma wasu na musu kallon cewa su shafaffu ne da mai, basu tabuwa, su ke sawa a yi, su ke sawa a bari a gidan gwamnati.

Sai dai duk abinda za’a fada game da wadannan mutane, babu wata kwakkwarar hujja na dauki daura dake nuna suna da hannu cikin kowacce irin badakala, asali ma sun kare shugaban daga jita jita da hasashe a lokacin da ya kwanta tsawon kwanaki 100 yana jinya a kasar Ingila.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel