Amfanin ruwa guda 10 a jikin mutum idan ya sha da safe kafin ya fara cin abinci

Amfanin ruwa guda 10 a jikin mutum idan ya sha da safe kafin ya fara cin abinci

- Ruwa dai bahaushe na kiranshi da abokin rayuwa kacokan

- Hakane kuwa, don amfanin ruwa ba ya kirguwa ga dan adam

- Shan ruwa da sassafe kafin cin komai na da matukar amfani da fa’idoji

A duk ayyukan ka na yau da kullum, jikinka na bukatar karfi. Wannan dalilin ne yasa kake shan ruwa don kashe kishi. Amma saboda wahalar yau da kullum, wasu kan manta da ruwan gaba daya. Amma kunsan cewa shan ruwa da sassafe na da matukar amfani?

Jikinka na bukatar ruwa kana tashi da sassafe. Kana tashi da safe, dauka kofin ruwanka ka sha kishi. Akwai tabbacin cewa zaka ga sauyi a yanayin lafiyarka cikin kankanin lokaci.

Ga wasu amfanin shan ruwa da sassafe daga tashi bacci kafin a ci komai.

1. Shan ruwa da sassafe na samarwa da jikin dan Adam karin ruwa, duba da irin sa’o’in da aka dauka ana bacci.

2. Shan ruwa kafin a ci abinci da safe na kara karsashi da karfin jiki.

3. Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tada kwakwalwa.

4. Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tsaftace jiki daga cutuka.

5. Shan ruwa da sassafe kafin a ci abinci na yakar cutuka tare da kara garkuwa ga jikin dan Adam.

KU KARANTA: Kaf kabilun Najeriya babu masu wulakanta matansu kamar Hausawa - Rabi Salisu

6. Shan ruwa da sassafe yana sa narkewar abinci kamar yadda ya dace.

7. Hakazalika, yana sa a rage kiba, ga masu muguwar kiba.

8. Yana gyara launin fata tare da sanya walwalin fata da walkiya.

9. Yana kariya daga ciwon koda tare da tsaftace mafitsara daga kwayoyin cuta.

10. Shan ruwa da safe kafin cin abinci na taimakawa tsawon gashin kai tare da walkiyarshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel