Kasa Ta Girma: Najeriya Za Ta Karbi Bakuncin Babban Taron Duniya da Za a Yi

Kasa Ta Girma: Najeriya Za Ta Karbi Bakuncin Babban Taron Duniya da Za a Yi

  • Najeriya za ta zama cibiyar taron ƙwararrun masu hulɗar jama’a na duniya na 2026, inda ake sa ran mahalarta daga ƙasashe sama da 126
  • Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce shirya taron zai ƙara fito da ƙwarewar Najeriya tare da buɗe sabbin damammaki
  • Shugaba Bola Tinubu zai karɓi baƙuncin taron, wanda za a haɗa da babban taron ƙungiyar APRA karo na 37 daga 15 zuwa 22 ga Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta fara shirye-shiryen karɓar dubban ƙwararru da wakilan ƙasashen duniya da za su halarci babban taron hulɗar jama’a na duniya na shekarar 2026 (WPRF) a Abuja.

Ana sa ran taron zai gudana tsakanin 15 zuwa 22 ga watan Nuwamba, inda mahalarta daga ƙasashe sama da 126 za su samu damar tattauna batutuwan da suka shafi sadarwa da hulɗar jama’a.

Kara karanta wannan

'Sai masu biyayya': An ware ƴan APC da za a ba motoci a kamfen Tinubu

Za a yi taron duniya a Najeriya
Ministan yada labarai, Mohammed Idris da wasu manya a ma'aikatar yada labarin yayin shirin karbar bakuncin babban taron duniya. Hoto: Khalid Ahmed/FMINO.
Source: Facebook

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai a Abuja wanda ma'aikatar ta wallafa a shafinta.

Ya ce shirya taron a Najeriya zai ba ƙasar damar nuna irin gudunmawar da za ta iya bayarwa wajen bunƙasa harkokin sadarwa a duniya, tare da faɗaɗa hulɗarta da sauran ƙasashe.

Najeriya ta samu damar karɓar taron a Afirka

Idris ya bayyana cewa Najeriya ta samu wani matsayi na musamman a tarihin gudanar da taron, domin ita ce ƙasa ta farko a Yammacin Afirka kuma ta biyu a nahiyar da za ta karɓi baƙuncin WPRF.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai jagoranci tarbar mahalarta taron a matsayin babban mai masaukin baƙi.

Baya ga taron WPRF, za a kuma gudanar da babban taron Ƙungiyar Hulɗar Jama’a ta Afirka (APRA) karo na 37 a lokaci guda.

A cewar ministan, haɗa waɗannan taruka biyu zai samar da damar tattaunawa kan makomar sadarwa tare da ƙarfafa rawar da Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ke takawa a wannan fanni.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da zai sa Obi ya gudu a Najeriya ko ya ci zaben 2027

Gwamnati ta jaddada muhimmancin gaskiya a sadarwa

Da yake magana kan babban jigon taron mai taken “Sadarwa Mai Haƙƙi: Muryar Duniya”, ministan ya yi kira ga masu sana’ar hulɗar jama’a da su mayar da gaskiya da sahihancin bayanai ginshiƙin aikinsu.

Ya ce bai kamata ƙwararrun wannan fanni su takaita ayyukansu wajen inganta sunan mutane ko cibiyoyi ba, domin suna da babban nauyin tabbatar da cewa jama'a suna samun bayanai masu inganci.

Ya kuma yi gargaɗin cewa yaɗuwar bayanan ƙarya da raguwar amincewar jama’a ga kafafen sadarwa na buƙatar ƙwararru su ƙara taka-tsantsan wajen isar da saƙonni.

A kalamansa:

“Dole ne ƙwararrun masu hulɗar jama’a su fahimci cewa nauyin da ke kansu ya wuce kula da martabar mutane ko inganta muradun cibiyoyi. Suna da haƙƙin tabbatar da gaskiya, sahihancin bayanai, bayyana gaskiya, bin ƙa’idojin sana’a da kuma kare muradun jama’a.”

Kowane dan kasa na amfana da Tinubu - Minista

An ji cewa Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce dukkan ’yan Najeriya na amfana da sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Ku sake zaɓen Tinubu': APC ta faɗi ɓangarori 4 da zai ba muhimmanci

Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da manufofin APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 mai taken “Daga Sauye-Sauye Zuwa Wadata”.

Minista Mohammed Idris ya ce mutane miliyan 1.6 na amfana da asusun lamunin karatu na NELFUND.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.