Allah Sarki: Bayan sun shafe shekara 7 suna tare ya gano cewa akwai wanda take so tun farko haka yasa ya saketa domin taje ta aure shi

Allah Sarki: Bayan sun shafe shekara 7 suna tare ya gano cewa akwai wanda take so tun farko haka yasa ya saketa domin taje ta aure shi

- Wani mutum ya garzaya gaban kotu a kasar India don neman a raba aurensu na shekaru 7 da matarshi

- Hakan ya biyo bayan son da ya lura matarshi na yi wa tsohon masoyinta wanda bata aura ba

- Duk da suna zaman lafiya kuma har da yara biyu, ya yanke hukuncin cewa ta je ta samu farin cikinta

Wani mutum ya nemi kotu ta rabashi da matarshi bayan da ya gano har a lokacin tana kaunar tsohon saurayinta da bata aura ba. Lamarin dai ya zama tamkar a wasan kwaikwayo.

Zaku iya tuna abinda ya faru a wani fim din kasar Indiya mai suna Hum Dil De Chuke Sanam? Jarumi Salman Khan ne da Aishwariya Rai, ke matukar kaunar juna. Amma sai dai kash, mahaifin Aishwariya ya mika aurenta ga Ajay Devgn. Amma da Ajay ya gano yadda matarshi ke kaunar tsohon suarayinta, sai ya yanke hukunci sada ta da masoyinta.

Amma daga karshe, Aishwariya ta yanke hukuncin rabuwa da Salman Khan tare da zama da mijinta Ajay Devgn.

A wannan lamarin kuwa, ba hakan bane ya faru. Mutumin dan asalin Bhopal ya auri matarshi ne kusan shekaru bakwai da suka gabata. Sun haifa ‘ya’ya biyu da shi.

Kamar yadda jaridar India Today ta bayyana, ma’auratan na zaman lafiya amma daga baya mijin ya gano babu wani farin ciki tare da matar. Tana son komawa wajen tsohon saurayinta.

KU KARANTA: Tashin hankali: Dalibin jami'a a Najeriya ya dankarawa malamar shi cikin shege

Daga karshe dai mijin ya kai al’amarin gaban kotu saboda yana son farin cikin matarshi. Ya yi iya kokarinshi wajen ganin matar ta hakura ta zauna dashi, amma ta fi kaunar tsohon masoyinta.

A don haka ne ya sanar da kotun cewa baya so hakan ta shafi ‘ya’yanshi, don haka yake neman saki. Har yanzu dai ana shari’ar. A halin yanzu dai mutumin ya bukaci a bashi rikon yaran, kuma matar ta yarda. Ya kara da amincewa a kan zata iya zuwa ganin yaran duk lokacin da ta so.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel