Kishi: Budurwa ta soki masoyinta da cokali mai yatsu bayan ta kama shi da cin amana

Kishi: Budurwa ta soki masoyinta da cokali mai yatsu bayan ta kama shi da cin amana

Wata budurwa mai suna Labake Olowokere, ta soki masoyinta mai suna Seun Komlafe da cokali mai yatsu sakamakon kama shi da tayi da wata budurwar.

An gano cewa, Labake ta ziyarci masoyinta Seun ne a yankin Okeopa da ke Ilesha wajan karfe 8 na dare, da niyyar daukar gas din girki. Anan ne ta tarar da wata budurwar a gidan.

Bayan farfadowa da tayi daga mamakin, Labake ta ja Seun da budurwar da fada. Rigima ta sarke wanda hakan yasa Labake ta dauko cokali mai yatsu tare da soka wa Seun a ciki, a take kuwa ya fadi ya mutu.

DUBA WANNAN: EFCC ta bankado laifin sanatan da ke son a kirkiri dokar amfani da dandalin sada zumunta

Mukaddashin mai magana da yawun jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar Osun, Mustafa Katayeyanjue, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Abiodun Ige, ya bada umarnin bincike a kan lamarin.

Ya ce, "Wajen karfe 10:30 na yammacin ranar Litinin, wani Adeyemi Ojo na titin Araromi ya kawo wa jami'an 'yan sanda karar wata Labake Olowokere ta Ido Ijesa. Ta soki masoyiinta Seun Komolafe na yankin Okeopa a Ilesha a ciki da cokali mai yatsu inda a take ya mutu,"

"Daga binciken farko, Labake ta isa gidan masoyinnata ne zata dauka gas din girki. Daga zuwanta sai ta tarar da wata budurwa tare da shi amma sai fada ya sarke," ya ce.

"A yayin wannan hatsaniyar ne ta dauko cokalin karfe ta soki Seun a ciki. A take kuwa ya rasa ransa. Tuni dai aka adana gawar mamacin a asibitin Wesley Guild da ke Ilsha." A cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel